Sabon Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS), Muhammad Nami, ya ragargaji wanda ya gada, Babatunde Fowler, cewa bai tabuka abin kirki ba a shekarun da ya shafe ya na shugabancin hukumar.
Nami ya ce tun da Fowler ya zama shugaban FIRS, maimakon a rika samun karin kudaden shiga, sai ma raguwa suka rika yi.
Wannan ne karo na farko da Nami ya yi wa ma’aikatan tara kudaden haraji, tun bayan kama aikin sa a ranar 19 Ga Disamba, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi.
Ya yi korafin cewa kudaden da FIRS ta tara tsakanin 2011 da 2012 har yanzu ba a tara kamar su a kowace shekara ba, a zamanin Fowler.
“Duk da cewa a lokacin shugaban FIRS da ya wuce, an dauki jami’an tara haraji masu zaman kan su, an kara ma’aikata kuma an samu hauhawar canjin kudi, hakan bai sa an tara kudade masu yawa a kowace shekara ba, kamar yadda aka taba tarawa tsakanin 2011 zuwa 2012.
” Dalili kenan a yanzu mu ka sa gejin kudaden da za mu rika tarawa a kowace shekara sai ya kai ko ya haura naira tiriliyan 5.7, kamar yadda aka taba tarawa a 2012.”
Daga nan sai ya jinjina wa ma’aikatan, tare da yin kira gare su cewa su dawo daga hutun Kirsimeti da na Sabuwar Shekara cikin shirin fara aiki tukuru.
“Matsayin a 2012 za a iya tara naira tiriliyan 5.7, babu dalilin da zai sa a yanzu ba za a iya tara adadin wadannan kudaden ba.” Inji Nami.