Har yau APC na nan da karfin ta gagau a Zamfara – Inji Yari

0

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya bayyana cewa har yau har gobe jam’iyyar APC na nan gagau da karfin ta a jihar, duk kuwa da sakacin subucewar mulkin da jam’iyyar ta yi daga hannun ta.

Yari ya bayyana haka a ranar Asabar da ta gabata, a lokacin da yake jawabi, lokacin da mabobin jam’iyyar daga Kananan Hukumomi 14 suka kai masa ziyara, a gidan sa da ke Talata-Mafara.

Yari ya kira taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC ne na jihar Zamfara.

Ya yi kira ga magoya bayan APC su ci gaba da hakuri tare da nuna biyayya ga hukuma da su kasance masu bin doka da oda.

“Mun gamsu da irin yawan magoya bayan da suka halarci wannan taro a yau; hakan na nufi da cewa har yanzu APC na nan da karfin ta gagau a jihar Zamfara.

“Ina kuma kara gode muku dangane da jajircewar da ku ke ci gaba da yi wajen goyon bayan APC,duk kuwa da irin manyan kalubalen da ake fuskanta.

“Ina tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da samar da kyakkyawan shugabanci da jagorancin jam’iyyar mu, domin samar da hadin kai da zaman lafiya.”

Kafin nan sai da shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Lawal Liman ya fara yin jawabin godiya ga Yari dangane da kokarin sa ta assara hadin kai a tsakanin magoya bayan APC a jihar Zamfara.

Daga cikin wadanda suka halarci taron har da shugabannin APC na dukkan kananan hukumomi 14 da tsoffin ‘yan majalalisar da suka yi wakilci a karkashin APC.

Idan ba a manta ba, cikin makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da tsohon Sanatan Zamfara, Kabiru Marafa na cewa, “Ba zan je taron sasantawar ‘shirmen’ da Yari ya shirya a Zamfara ba.”

Tsohon Sanatan Jihar Zamfara, Kabir Marafa, ya nesanta kan sa daga taron neman sasantawa da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya shirya yi da gungun ‘yan jam’iyyar APC ‘yan G-8 din da ya samu sabanin siyasa da su kafin zaben 2019.

Kakakin Yada Labarai na APC reshen Jihar Zamfara, Shehu Isah, ya shaida wa manema labarai a Gusau cewa wannan kungiyar ta G-8 ta yunkuro da nufin sasanta kazamin rikicin da ya tirnike har ya haddasa APC ta rasa dukkan mukamai a zaben 2019 na jihar Zamfara.

Kungiyar Mashahuran G-8 na Zamfara, sun hada da Kabiru Marafa, Dauda Lawal, Ibrahim Wakkala, Mahmud Shinkafi da Aminu Sani da sauran su.

Ya ce sun tattauna matsalolin da APC ta fuskanta a lokacin hauma-haumar zaben 2019, kuma sun cimma amincewar zama su magance matsalolin.

Sai dai kuma a na sa bangaren, Marafa ya ce shi dai ba ya “cikin wannan kwaram-da-hama da sunan taron sasantawa.”

Sannan kuma ya ce shi dai babu wanda ya sanar da shi akwai wani taron sasantawa, kuma ko da an sanar da shi din, to bai ga dalilin zuwa ba.

Marafa ya ce tun farko Yari ne ya ki amincewa a zauna a magance matsalar tun kafin zabe, duk kuwa da kokarin da uwar jam’iyya, fadar shugaban kasa da manyan ‘yan siyasa suka yi domin jawo hankalin sa.

Marafa ya ce a lokacin Yari ya na jin kan sa, ya na tutiya da tinkahon cewa shi ne gwamnan Zamfara, kuma ya na da kudaden Zamfara na da Kungiyar Gwamnonin Najeriya a hannun sa, sai yadda ya ga dama ya rika yi.

“A lokacin ya je ya samu hukuncin baubawan-burmi daga Kotun Jiha, wanda Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli suka yi fatali da shi.

“A yanzu kuma ya ga ba shi da karfin mulki a hannun sa, Allah ya wofintar da shi, jama’a kuma sun juya masa baya, shi ne a yanzu ya ke ta kokarin shirya wani taron ihu-bayan-hari, domin ya sake farfado da tagomashin sa.

“Tun farko shi ne ya ki yarda ya saurari kiraye-kirayen da jama’a masu tunani da hangen nesa suka rika yi masa, wanda da a lokacin ya tsaya ya saurara, da shawarwarin sun amfani jama’ar mu da jam’iyyar mu baki daya.” Inji Marfa.

“Yari ne ya haifar da dukkan matsalolin da suka haifar wa APC mummnunar asara a Jihar Zamfara, saboda ya rika daukar kan sa wani ubangiji, mai girman kai, saboda kawai tantagaryar jahilci ya yi masa katutu. Alhali kuwa ba komai ba ne, kuma ba kowa ba ne. Dama holoko ne, kuma tubalin-toka.”

Share.

game da Author