Gwamnatin jihar Nasarawa na kashe naira miliyan 240 duk wata don inganta kiwon lafiya

0

Shugaban asibitin ‘Dalhatu Araf (DASH) dake Lafiya jihar Nasarawa, Hassan Ikrama ya bayyana cewa a duk wata gwamnatin jihar na kashe Naira miliyan 240 wajen inganta kiwon lafiya a jihar.

Ikrama ya fadi haka ne da yake ganawa da manema labarai a garin Lafiya.

Ya ce gwamnati na amfani da kaso mai tsoka daga cikin wannan kudi wajen ganin mata masu ciki, yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar da tsofaffi na samun kula kyauta a asibitocin gwamnati dake jihar.

Sannan sauran kudaden ana amfani da su wajen horas da ma’aikata da biyan su albashi.

Ikrama yace a dalilin ayyuka da gwamnati ta yi a asibitin jihar ya roki mutane da su rika zuwa asibiti domin ana duba su .

Idan ba a manta ba a watan Nuwamba ne karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu muhimman matakai domin rage yawan mace-macen jarirai da mata a Najeriya.

Mamora ya ce ya zama dole a samar da manufofi da za su taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara ganin cewa bincike ya nuna cewa mata 576 daga cikin mata 100,000 ne ke mutuwa sannan yara 37 daga cikin 1000 ne ke mutuwa a Najeriya duk shekara.

Ya ce gwamnati a shirye take domin hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiyar kasan domin kawar da wannan matsala.

Share.

game da Author