Gwamnatin Jihar Kano ta Janye dokar haramta wa mace da namiji shiga Keke NAPEP daya

0

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta janye dokar haramta wa mace da namiji shiga Keke NAPEP da ake kira adaidaita sahu.

Kakakin Hukumar Hisbah, Lawan Fagge ne ya sanar da haka ranar Talata inda ya kara da cewa gwamnati ta yi haka ne a dalilin neman karin lokaci da kungiyar matuka adaidaita sahu suka nema daga gwamnati.

Ya ce yanzu dai an dakatar da wannan doka. Fage ya idan gwamnati ta kammala duba tsarin dokar za ta sanar wa mutane matsayinta.

Gwamnati ta sanar cewa da ga 1 Ga Janairu dokar zata fara aiki.

Tun bayan bayyana wannan doka ne, mutane suka yi ta caccakar gwamnati da nuna rashin amincewar su game da haka.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka a lokacin da ake rufe wani taron sanin makamar aiki, IVC na Musulunci, wanda Kungiyar Dalibai Musulmi ta Shiyya, ta shirya a Jami’ar Bayero, Kano, ranar Laraba.

Kwamandan Hisba, Harun Ibn-Sina ne ya wakilci Ganduje a wurin taron, kuma shi ne ya yi sanarwar a wurin taron.

Ya ce Jihar Kano ta hana daukar mace da namiji a lokaci guda a cikin A Daidaita Sahu, ba a cikin birnin Kano kadai ba, har ma da dukkan sauran kananan hukumomi 44 na jihar baki daya.

Idan ba a manta ba, an shigo da keken A Daidata Sahu a matsayin keken sufurin haya mai daukar mata kadai, a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau. Kuma tun a wancan lokacin ne aka sa masa sunan A Daidaita Sahu.

Gwamnatin Shekarau ta shigo da keken A Daidaita Sahu ne bayan ta haramta haya da babur.

A wurin taron dai Mai Martaba Sarkin Kano ya kara jan hankalin Musulmi su daina daukar hidimar abin da ya fi karfin su ko ka fi nauyin aljifan su.

Daga nan sai ya danganta yawaitar yara kanana da ke gararamba ba su zuwa makaranta, cewa yawan aure-auren mata da tara iyalin da namiji bai iya daukar nauyin su ne ke kara yawaitar irin wadannan yaran.

Share.

game da Author