Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba za ta tsaya wani bata lokaci ba wajen dakatar da duk wani ma’aikatacin N-Power da aka kama ya na kin zuwa wurin aikin da aka tura shi.
Manajan yada labarai na Ofishin SIP, Justice Bibiye ne ya bayyana haka a Abuja, bayan da rahotannin da ofis din ya samu sun tabbatar cewa ma’aikata da dama na karbar kudin N-Power ba tare da zuwa aiki a wuraren da aka tura su ba.
Bibiye kua ya kara da cewa alamu sun nuna tabbas wasu masu karbar alawus din Naira 30,000 na N-Power kan dauki lokaci mai tsawo ba su je aiki ba.
Idan ba a manta ba, a cikin watan Yuli. 2019, PREMIUM TIIMES ta wallafa labarin yadda ma’aiakatan N-Power ba su zuwa aiki a jihohin Adamawa, Kano da kuma Katsina.
Ita kuma hukumar SIP, mai kula da N-Power, sai ta kori sama da mutane 2,500.
SIP ta kara yin sanarwar cewa kimanin masu cin lawus din N-Power su 18,674 ne suka ajiye aikin su, bayan da suka samu aikin dindindin.
Daga nan ya bayyana cewa sun fara sa-ido kan ma’aikatan N-Power da ake turawa makarantu koyarwa a jihohi daban-daban, a karkashin shirin hada-ka tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin Jiha.
Ya ce an dade ana samun korare-korafen rashin zuwa aikin da yawa daga masu amfana da N-Power. Amma yanzu gwamnati za ta kara daukar tsatstsauran mataki kan wannan fashi da suke yi.