Gwamnati za ta gina dakunan bahaya na naira miliyan 60 a jihar jigawa

0

Kwamishinan ruwa na jihar Jigawa Ibrahim Hannun-Giwa ya bayyana cewa gwamnati ta ware akalla naira miliyan 60 domin gina dakunan bahaya a jihar.

Hannun-Giwa ya fadi haka ne ranar Laraba a ziyarar da ya kai fadar sarkin Hadejia Adamu Abubakar-Maje

Ya ce za a gina dakunan bahayan ne a makarantu, asibitoci, tashar motoci da kasuwani a kananan hukumomin Auyo, Gagarawa da Kiyawa.

“ Gwamnati ta yi haka ne domin ganin ta hana yin bahaya a waje a jihar.

“ Idan ba a manta ba bincike ya nuna cewa Najeriya ce kasa ta biyu da duniya da yin bahaya a waje ya yi wa katutu.

Hannun -Giwa ya yi kira ga masarautar da ta hada hannu da gwamnati domin samun nasarar wannan aiki da suka saka a gaba.

Bayan haka a tsokacin da ya yi Abubakar-Maje ya ce masarautar Hadejia za ta mara wa gwamnati baya dari bisa dari domin ganin an kawar da wannan matsala a jihar.

Ya ce za a yi sanarwar illollin dake tattare da yin bahaya a waje tare da jaddada wa mutane hukuncin karya dokar yin bahaya a waje a duk garuruwan masarautar sa.

A karshe shugaban karamar hukumar Auyo, Umar Musa-Kalgwai ya mika godiyarsa ga gwamnatibisa wannan mataki da ta dauka na gina dakunan ba haya da kuma kokarin ilmantar da mutane illolin dake tattare da yin bahaya a waje ko kuma a ko-ina.

hana yin bahaya a waje musamman yadda yin haka zai taimaka wajen kare kiwon lafiyar mutane daga kamuwa da cututtuka.

Share.

game da Author