Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar fara biyan kudin abinci da biyan masu dafa abincin ciyar da ‘yan firamare na 2020 a jihohi 33 da FCT, Abuja.
Wannan bayani ya fito daga bakin Ministar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq.
Sadiya ta ce an fara biyan kudin ne tun yanzu q cikin watan Disamba, domin a fara ci gaba da aikin dafa abincin ciyarwar gadan-gadan da an koma karatu a farkon Janairu, 2020.
Cikin wani jawabi da Minista Sadiya ta aiko wa PREMIUM TIMES, ta ce ba a son samun wata matsala ko cin karo da wani cikas ko kadan, shi ya sa aka fara biyan kudaden ga masu dafa abincin domin su fara tanadin sayen kayan abincin da wuri.
Daga nan kuma ta yaba da tahotonnim da ta ke samu cewa sakamakon ciyar da ‘yan firamare da gwamnatin tarayya ke yi, a yanzu ana samun yawan kara tura yara makarantun firamare kuma su ‘yan makarantar su na kara kulawa da tsafta sosai.
Ta ce dama makasudin shirin kenan, domin a kara samun ingancin ilmi.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fito da shirin ciyarwa ga ‘yan firamare cikin 2016. Shirin na cikin tsarin amfani da naira bilyan 500 domin inganta rayuwar al’umma, SIP.
Gwamnati ta yi shirin da zimmar samar da aiki ga mutane milyan 1.14. An fara shirin a karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, amma cikin 2019 aka maida shirin a karkashin ofishin Minista Sadiya.
Wani daftari da Gwamnati ta fitar cikin 2019 ya nuna ana ciyar da ‘yan firamare sama da milyan 9 a jihohi 30, makarantu 52,604. Sannan kuma akwai masu dafa abinci har su 101, 913 da ake biyan su kudin abincin da na aikin su kai tsaye a asusun bankin kowanen su.