Gwamna Zulum ya umarci cibiyar kula da masu fama da cutar koda ta rika duba mutane kyauta

0

Gwamna Babagana Zulum na jihar Barno ya umarci cibiyar kula da masu fama da cutar koda ta rika duba mutane kyauta a jihar.

Zulum ya bayyana haka ne da a yayin ziyara da ya kai babban Asibitin jihar inda cibiyar take.

” Maimakon a rika karbar kudaden talakawa da ke fama da cutar, za a rika duba su kyauta a duk lokacin da suka garzayo a duba su.

A duk lokacin da mai fama da cutar ya tafi asibiti neman magani sai ya biya naira N30,000. Haka kuma idan lokacin duba shi ya sake zagayowa sai ya kara biyan wadannan kudade. Daga yanzu dai hakan ya kare a jihar Barno domin Zulum ya ce a rika duba su kyauta.

Gwamna Zulum ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da samarwa mutanen jihar ababen more rayuwa da kula da inganta kiwon lafiyar su a jihar.

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Salisu Kwaya-Bura da ya zazzagaya da gwamna Zulum cibiyar ya ce sun karo kayan aiki da dama domin a sumu damar iya kula da mutanen dake fama da cutar har na tsawon watanni shida ba tare da an samu matsala ba.

A karshe Zulum ya umarci kwamishina Salisu da ya zakulo dalibai masu hazaka domin aikawa da su cibiyoyi da makarantun koyarda yadda ake yin musanyar koda domin a fara yi a asibitocin jihar.

” A duba wadannan wurare ko a kasarnan ko kuma ma idan a kasashen waje sai a tura su.”

Share.

game da Author