Babban Mai Taimakawa Ga Shugaba Muhammadu Buhari Kan Yada Labarai, ya nuna goyon bayan kokarin da Majalisar Dattawa ke yi na kakaba wa soshiyal midiya doka.
Garba Shehu ya bayyana wannan goyon bayan ne a wurin Bukin Bada Kyaututtuka na farko da jaridar Kwararafa Reporters ta shirya.
Shehu ya ce idan ba a yi wa soshiyal midiya daurin talalar dokokin watsa sakonni ba, to za su haifar da karya dokoki, rashin bin doka, hargitsi da kuma kashe-kashe.
Sai dai kuma Shehu ya ce don Gwamnatin Najeriya na so a yi wadannan dokokin, ba wai ta na yaki da ‘yancin fadin albarkacin bakin jama’a ba ne.
“Kafafen yada labarai na zamani su na da karfin yada sakonni da saurin kai bayanai su watsu ko’ina a duniya. Kuma sun karfafa dimokradiyya. Amma idan ba a kulawa da sa-ido sosai a kan su, to za su haddasa hargitsi sosai.”
Ya buga misali da yadda soshiyal midiya ta zama alakakai a kasar Birtaniya, inda ta haddasa matasa shan sigari sosai.
Sannan kuma Shehu ya kara da cewa, soshiyal midiya ce ta haddasa wani kashe-kashen mutane sama da 50 da aka yi a kauyen Kasuwar Magani, cikin Jihar Kaduna, kamar yadda Maitaimakin Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, mai suna Attah Esa ya bayyana.
Jama’a da dama na nuna rashin goyon bayan kafa wannan doka, yayin da gwamnati ke nuna yadda ake yada labaran kiyayya a soshiyal midiya.
Cikin wadanda suka yi kotafi kan soshiyal midiya a kwanan nan, har da Aisha Buhari, Maidakin Shugaba Mushammadu Buhari, wadda ta ce ita ma soshiyal midiya ta dagula mata lissafi kwanakin baya.
Shekaru uku da suka gabata ne aka kafa Kwararafa Reporters, a Abuja, wadda jarida ce ta Online.
A wurin bada kyautukan dai an bai wa Garba Shehu da Babban Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Femi Adesina.
Discussion about this post