A karo na biyu, gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sake aikawa da kudirin kirkiro sabbin masarautu hudu a jihar zuwa majalisar dokokin jihar.
Kwamishinan yada labarain jihar Kano, Muhammad Garba, ne ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Garba ya ce tun bayan kotu ta soke sabbin masarautun a bisa wasu dalilai da ta ce ba a yi daidai ba a kan su, gwamnati ta sake zama domin sake aika wa da kudirin kirkiro da sabbin masarautun sannan a yau Litinin, ta aika wa majalisar Jihar.
Idan ba a manta ba Kotu ta rusa masarautu hudu da Ganduje ya kirkiro cewa gwamnati bata bi ka’ida ba wajen kirkiro su.
” Ina so ku sani cewa, wasu masarautun da aka kirkkiro sun fi masarautar Kano asali da dadadden tarihi. Sun kafu tun kafin masarautar Kano. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa muke so mu dawo wa wadannan masarautu ikon su da martaba.
” An taba kokarin kirkiro irin wadannan masarautu amma ba su dore ba, a yanzu gwamnatin Ganduje na so ta ga hakan ya tabbata sannan sun tsayu gidigam.
Garba ya ce bayan haka anyi gyara ga dokar d masarautun Kano domin kawo ci gaba a jihar ne sannan ya yi kira ga majalisar dokokin jihar da su gaggauta kammala aiki a kai domin ba gwamnati damar kirkiro wadannan masarautu.
Masarautun da za akirkiro sun hada da Masarautar Rano, Gaya, Bichi da Karaye.
Discussion about this post