GABAR CIKIN GIDA: Yadda Kasimu ya yi garkuwa da kanwarsa Asiya ya bukaci mahaifin su ya biya Miliyan 10

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wani matashi mai suna Ibrahim Kasim dake da shekara 22 wanda ta kama da laifin yin garkuwa da kanwarsa da suke uba daya sannan ya nemi mahaifinsu ya biya kudin fansa.

Kasim ya aikata haka ne a kauyen Makera dake karamar hukumar Funtua ranar 16 ga watan Nuwamba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Gambo Isah yace Kasim ya yi garkuwa da Kanwarsa mai suna Asiya ‘yar shekara shida. Kasimu ya aikata haka da taimakon budurwarsa Murja da wasu abokan sa.

” Daga nan sai Kasim ya rika amfani da abokanan sa da shi kansa suna kiran mahaifin sa cewa ya biya Naira Miliyan 10 kudin fansa na garkuwa da Asiya da suka yi ko kuma su kashe ta, shi ko mahaifin bai sani cewa dan sa bane.

Yanzu dai Kasimu na tsare a hannun ‘yan sanda bayan cafke shi da suka yi sannan ana nan ana ci gaba da bincike akai.

Idan ba manta ba rundunar ta cafke wata mata mai suna Aisha Abubakar mai shekaru 38 da aka kama da laifin kashe ‘yar kishiyarta ta hanyar zuba mata guba a abinci.

Isah yace Aisha ta aikata wannan mummunar abu ne ranar 28 ga watan Nuwamba a gidan mijinta dake kwatas din Sabuwar – Unguwa karamar hukumar Rimi.

Ya ce a wannan rana dai an watse ne daga gida aka bar Aisha da ‘yar kishiyar ta ‘yar shekara hudu.

Da Aisha taga babu kowa a gida sai ta dauki guba ta zuba a cikin abincin wannan yarinya sannan ta tilasta ta taci. Daga nan ne fa yarinya ta yanke jiki ta fadi kasa. ” Ko da aka kai ta asibiti, sai tace ga garin ku nan.”

Isah ya ce da aka yi bincike ne aka gano cewa wannan mata wato Aisha da gangar ne ta kashe wannan yarinya saboda tsananin kishi da take yi da uwarta.

Har yanzu ‘yan sanda na ci gaba da bincike akai. ” Idan muka gama zamu gurfanar da ita a gaban kotu.

Share.

game da Author