Ko shakka babu Shugaba Muhammadu Buhari ya bar tsohon Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji, Babatunde Fowler cikin mamaki da faduwar gaban jin yadda aka bayyana sunan wanda zai maye gurbin sa a ranar Litinin.
A ranar Litinin din ne Fowler ya rubuta wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha wasikar neman alfarmar a bar shi ya karasa wasu shekaru hudu a shugabancin FIRS, “domin kara ingantawa da gina muhimman nasarorin da ya samar.”
Haka ya rubuta a cikin wasikar, wadda ya aika, amma sa’o’i kadan bayan aikawa da wasikar, sai kawai ya ji an bayyana sunan wanda zai maye gurbin sa.
Wasikar Fowler, wadda yanzu haka akwai kwafen ta a hannun PREMIUM TIMES da ya aika jiya 9 Ga Disamba, ranar da wa’adin shekarun sa hudu na shugabancin FIRS ke cika, an bi ta da kullin sanar da nada Muhammadu Nami da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a FIRS.
Bayan cire Fowler da aka yi a ranar Juma’a, nan take ya yarda da kaddara, har ya gode wa Shugaba Buhari, tare da cewa, “babu wani tabbas dangane da batun zarcewa zango na biyu din aikin da aka bai wa mutum ya yi,” haka ya bayyana wa abokan aikin sa, kamar yadda kakakin FIRS, Wahab Gbadamosi ya bayyana.
Sai dai kuma duk da Fowler ya san neman zarcewa zango na biyu ba abu ne mai tabbas ba, hakan bai hana shi neman a kara masa shekaru hudu ya ci gaba da shugabancin FIRS ba.
Neman Alfarma
A cikin wasikar da ya aika, Fowler ya sanar da cewa wa’adin shekarun sa hudu sun cika, amma dai ya na neman alfarmar a kara masa wasu shekaru hudun.
“Na rubuto wannan wasika domin na sanar da Sakataren Gwamnatin Tarayya cewa wa’adin shugabanci na a FIRS ya cika a yau, 9 Ga Disamba, 2019.
“Dangane da haka ne, na ke gabatar da kai na domin a sake nada ni zango na biyu. Wannan na daga cikin tsarin Dokar FIRS TA 2007, wadda ta bada damar ana iya sake nada wanda ke kai ya sake wasu shekaru hudu.
“Hakan zai ba ni damar ci gaba da karfafawa da gina nasarorin da na samar a shekaru hudun da na rike hukumar.” Haka Fowler ya rubuta.
Dukan Biri Da Rani
Hausawa na cewa wai ‘da aka doki biri da rani, sai ya ce ya san dalili, barnar da ya yi da damina ce ta janyo masa.’
Idan ba a manta ba, watannin baya kafin Fowler ya nemi a sake nada shi, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari ya rubuta masa takardar nuna rashin godiya da gamsuwa da irin kokarin da ya ke yi wajen tara harajin kasar nan.
Cikin watan Agusta ne Fadar Shugaban Kasa ta rubuta masa waskikar, wacce Abba Kyari ya aa wa hannu.
Wasikar dai na dauke da rashin godiyar yadda harajin da ake tarawa a kasar nan ke kara yin kasa, tun daga 2015 bayan nada Fowler shugabancin Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida, wadda a Turanci aka sani da Federal Inland Revenue Services, ko FIRS a takaice.
An rubuta masa wannan wasikar rashin godiya a ranar 8 Ga Agusta, 2019.
PREMIUM TIMES ta binciko cewa cikin 2015 bayan nada Fowler, FIRS ta yi kirdadon samun kudaden shiga har naira tiriliyan 4.7, amma daga karshe dai hakan bai samu ba, sai naira tiriliyan 3.7 aka tara a shekarar.
Cikin 2018, an yi kirdadon cewa za a tara naira tiriliyan N6.7, amma hakan bai samu ba, sai naira tiriliyan 5.3 aka tara.
Damuwar da Fadar Gwamnatin Tarayya ta yi a kan hakan ne ya sa aka rubuta wa Fowler wasikar rashin godiya, tare da umartar sa cewa ya bayyana dalilin wannan wawakeken gibin da ake samu a kowace karshen shekara wajen kudaden harajin da ake tarawa.
An Roro, Sun Rore
An aika wa Fowler wasika ce kwanaki kadan bayan jami’an EFCC sun damke wasu jami’an FIRS sun tsare su tsawon kwanaki da dama, a wani binciken harkallar da aka bankado a hukumar.
A amsar da Fowler ya bayar, ya danganta karancin kudaden haraji da faduwar darajar farashin danyen mai, wadda ta haifar da faduwar daraja wasu kayayyaki da kuma matsin tattalin arzikin da kasar nan ta afka daga 2015 zuwa 2017.