FATATTAKAR BOKO HARAM DAGA DAMATURU: Buni ya jinjina wa dakarun Najeriya

0

Gwamnan jihar Yobe Mala Buni ya jinjina wa dakarun Najeriya bisa fatattakar Boko Haram da suka yi a kokarin far wa garin Damaturu da suka yi ranar Labadi.

Buni ya bayyana cewa wannan kokari da dakarun tsaron Najeriya suka yi ya cancanci yabo da jijinawa.

A takarda wanda kwamishinan yada labarai na jihar Yobe Abdullahi Bego, ya fitar a garin Damaturu ta ce gwamnan ya yi kira ga illahirin mutanen jihar da su dage da yin addu’o’in Allah ya kawo karshen wannan tashin hankali da ake fama da shi.

” Dole sai gaba dayan mu mun koma ga Allah sannan mu dave da yin addu’o’i Allah ya shiga tsakanin mu da wadannan mutane.

” Kowanne Addini kake bi, mu dage da addu’o’i kuma ina kira ga mutanen jihar su zauna lafita da juna da kuma mara wa jami’an tsaro gaba abu da suka sa a gaba na kawo karshen wannan matsala.

Idan ba a manta ba, a ranar Lahadi ne Bomo Haram suka nemi far wa babban birnin jihar Yobe.

Cikin mutane ya duri ruwa, kowa ya zauna cikin fargaba.

Mazauna garin Damaturu sun bayyana cewa rugukin harsashin bindiga kawai suka rika ji a wajen garin Damaturu ranar Lahadi a lokacin da Boko Haram suka yi kokarin far wa garin.

Sai dai hakan bai dade yana faruwa ba, dakarun sojojin Najeriya na kasa da Sama suka rika yi wa Boko Haram din luguden wuta sannan suna surfafar su ta kasa da manyan makamai har Allah ya basu nasarar fatattakar Boko Haram din.

Gwamnan Buni yana kasar Saudiyya wajen yin aikin Umrah.

Share.

game da Author