Fashewar bututun mai a kusa da Rukunin Gidaje na Gloryland Estate, da ke cikin Karamar Hukumar Egbe-Idimu, a jihar Lagos ta firgita jama’a da dama mazauna yankin.
Mazauna yankin sun rika tura faifai bidiyon yadda wutar ke ci da kuma jama’a na ta gudun tsira da rayukan su.
Wutar da tashi dai ta yi ta’adi har a cikin Rukunin Gidaje na Diamond Estate da ke kan hanyar Isheri/Lasu-Igando.
Har zuwa lokacin buga wannan labari dai ba a san takamaimen abin da ya haddasa wutar ba, amma dai mazauna yankin sun fi danganta ta da barayin mai masu fasa bututu.
Sannan kuma zuwa yanzu ba a tantance yawan wadanda wutar da ta tashi sanadiyyar fshewar bututun ta shafa ba.
Tuni dai aka kai jami’an kashe gobara da na ceton rayuka.
Dukkan kokarin da aka yi don jin ta bakin ofishin LASEMA, amma ba a yi nasara ba.
Ba wannan ne karo na farko da barayin mai masu fasa bututu ke haddasa gobara ba. domin hakan ta sha faruwa ana samun asarar rayuka da raunuka da kuma asarar dimbin dukiyoyin jama’a.
Discussion about this post