Duk Da Jinkirin Biyan ‘Yan Npower Akan Lokaci, Tabbas Gwamnatin Najeriya Ta Cancanci Yabo, Daga Mustapha Soron Dinki

0

A zance na gaskiya, a madadin duk matashin da Allah ya taimakeshi ya samu shiga cikin shirin gwamnatin tarayya na Npower.

Tabbas, sai mai rabo ne zai gwada neman abu a cikin miliyoyin mutane ya sameshi. Mun godewa Allah da wannan babbar kyauta.

Gwamnatin Najeriya tayi kokari matuka, yadda ta fitar da matasa masu karatu guda dubu dari biyar daga cikin kangin fatara ta rashin aikin yi.

Wadannan matasa an daukesu ne don suyi aikin kwantiragi na shekara biyu, wanda muke fatan zai zama aikin din-din-din insha Allah.

Duk da ‘yan wasu matsaloli kadan da ake fama dasu a cikin tsarin, mun yaba yadda gwamnatin Najeriya ta dauki aikin da kuma yadda ake tafiyar da tsarin har zuwa yanzu, a lokacin da wasu marasa kishin talaka suke ta fada da tsarin a bayyane.

Sannan kuma a wani bangaren, ‘yan uwanmu matasa wadanda Allah bai basu ikon shiga cikin tsarin ba suna shiga rigar wadanda suke cin moriyar shirin suna bata ingancin abun. Wannan kuskuren gaske ne, a rayuwa duk abunda aka fara idan kabi a hankali zai iya zuwa kanka idan da rabo. Illar ace ba a fara ba.

Komai lokaci ne, idan ba qaddara ba, ai babu matashin da zaka samu mai shekara talatin da biyar da digiri biyu ko uku (digiri, digirgir da dingirewa) amma yana aikin dubu talatin a wata. Komai a hannun Allah yake, a rokeshi idan yaso zai bayar.

Muna rokon gwamnati data kara inganta tsarin, ta hanyar warware matsalar rashin biya akan lokaci. Tabbas hakan zai samar da manufar da ake bukata.

Sannan su kuma ‘yan uwanmu da suke cikin shirin suyi kokari su riqe amana kuma su yi tunani akan rayuwarsu ta gaba saboda wannan rayuwar babu tabbas.

Gaskiya nayi farin ciki rannan da naga wani matashi ya kusa kammala digirinsa bayan an daukeshi Npower da kwalin NCE. Wannan ma cigaba ne a tunanina tunda ilimi shine babban jari (Investment)

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author