A sakamakon zaben da hukumar zabe ta fidda a daren Asabar bayan kammala zaben da aka yai a wasu rumfunan zabe 53, Adeyemi Smart ne ya lashe zaben.
Adeyemi Smart na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar sanata dake wakiltar Kogi ta Yamma.
Sanata Dino Melaye ne ke kan wannan kujera kafin kotu ta rusa zaben da ya kai shi wannan kujera.
Smart na APC ya samu kuri’u 88,373 inda Dino na jam’iyya APC ya tashi da kuri’u 62,133.
Yanzu dai kamar yadda sauran makusantarsa irin su sanata Bukola Saraki suka rasa kujerun su shi ma ta fado kan sa. Sai dai kuma har yanzu yana da damar garzaya kotu domin mika koke-koken sa da bin hakkin sa idan bai gamsu ba.
Idan ba a manta ba Hukumar zabe ta bayyana cewa zaben kujerar sanata na Kogi ta Yamma bai kammalu ba.
Malamin zabe da ya bayyana sakamakon zaben ya bayyana cewa kuri’un da aka soke sun fi yawan kuri’un da Adeyemi Smart ya lashe zaben da shi.
Shi dai Smart na jam’iyyar APC ya fi yawan kuri’u a zaben. Ya samu zunzurutun kuri’u 80,118, shi kuma Dino na PDP ya samu kuri’u 59,548.
Smart ya ba Dino ratar kuri’u 20,570.
A wannan lokaci ne shi kansa malamin zabe ya bayyana cewa an samu matsaloli a rumfuna 53 da ke da yawan wadanda suka yi rajistar zabe 43,127.
A bisa wannan dalili ya sa ba za a iya bayyana Smart da ya ke da yawan kuri’u a matsayin wanda yayi nasara a zaben ba.