Dan Majalisar Tarayya bai goyi bayan yi wa Majalisa kwaskwarimar naira bilyan 37 ba

0

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Ede ta Arewa, Ede ta Kudu, Egbedore da Ejigbo na Jihar Osun, ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kasafin kudin da Majalisa ta cusa na son kashe naira bilyan 37 wajen yi wa majalisar kwaskwarima.

Bamidele Salam, wanda tsohon dan jarida ne, ya bayyana a shafin sa na Facebook, inda ya nuna rashin cancantar kashe kudaden wadanda ya ce sun wuce hankalin mai hankali.

A jiya Lahadi ne ya yi wannan bayani a shafin sa, kuma daga baya ya kara tabbatar wa PREMIUM TIMES da wannan matsaya ta sa da ya dauka.

“A matsayi na na Dan Majalisa, wanda kuma ya san halin da ta ke ciki, ba na ganin cewa akwai bukatar kashe wadannan makudan kudade wajen wai yi wa Majalisa kwaskwsrima da naira bilyan 37.

” Banda bangaren sauraren sauti da kuma bangaren yin rikodin, ni dai ban ga wani wuri da ke bukatar kwaskwsrima ba.” Inji shi.

Ya ce da a kashe wadannan kudade ga kwaskwsrima, har ma gara a raba wa matasa guda 370,000 kudin. Kenan ya ce kowa zai tashi da naira 100,000 wadda za a baya shi a matsayin lamuni.

Ya ce yin hakan zai fi zama alheri. Tare da karawa da cewa kudaden da aka ware domin kwaskwarima a Fadar Shugaban Kasa da sauran ofisoshin manyan ‘yan siyasa, kamata ya yi a zabtare su, yadda za a iya tara wasu naira bilyan 250 da za a iya kara inganta masu kananan masana’antu a kasar nan.

Bamidele ya ce abin da zai sa gaba shi ne ya yaki wannan nufi na kashe wa Majalisa naira bilyan 37.

An dai cusa wadannan makudan kudade a cikin Kasafin FCT, Abuja. Wato ba su cikin zunzuritun kasafin Majalisar Dattawa da ta Tatayya na 2020.

Shi kuwa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya kare kudaden tare da bayyana cewa akwai wurare da yawa a Majalisa da ke bukatar a yi wa kwaskwarima.

Tuni dai ‘yan Najeriya suka nuna rashin amincewa a kashe kudaden. Kungiyoyin Kare Dimokradiyya sun fito sun ce ba su yarda a yi wan

Share.

game da Author