DALLA-DALLA: Dalilai 12 da ya sa kotu ta tura ‘Dan-Baiwan Kasar Hausa’ Uzo Kalu kurkuku

0

A yau Alhamis ce Mai Shari’a Mohammed Idris na Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ya daure tsohon gwamnan jihar Legas, Orji Uzor Kalu shekaru 12 a kurkuku.

An samu Kalu da laifin karkatar da naira bilyan 7.65 zuwa aljihun sa.

Ga Yadda Aka Yanke Masa Hukunci Nan:

1. An yanke wa Kalu daurin shekaru 12 a kurkuku.

2. An daure abokin harkallar sa, Udeh Udeogu shekaru 10 gidan kurkuku.

3. Mai Shari’a ya umarci gwamnati ta kwace kamfanin Kalu, Slok Nigeria Limited, ta sayar da kadarorin kamfanin, sannan a zuba kudin aljihun gwamnati.

4. An kama Kalu da aikata laifuka har 39.

5. Shekaru 12 kenan ana tabka wannan shari’a, sai yau aka karkare ta.

6. Tuni an yi gaba da su Kalu kurkuku, inda zai shafe shekaru 12, sai fa idan ya yi nasarar daukaka kara a Kotun Daukaka Kara ko Kotun Koli. Ko kuma ya samu sassaucin rage masa yawan shekarun zaman kurkuku.

7. An samu Kalu da laifi a dukkan zarge-zarge ko tuhume-tuhume 39 da aka yi masa.

8. Mai Shari’a ya ce EFCC ta gudanar da bincike tare da tabbatar da an aikata laifin.

9. Mai Shari’a y ace EFCC ta yi aiki wajen tabbatar da laifi a kan Kalu, ba tare da ta rage wani gibin da zai iya kawo takoke, shakku, tababa ko tawaya ga bincike da hujjojin su ba.

10. Kalu ya nuna kasawar sa wajen iya rike amanar al’ummar da aka damka masa.

11. Laifin da ya yi inji Mai Shari’a, ya karya dokar kama aiki a Najeriya, kuma abu ne da tilas sai an hukunta wanda ya yi irin haka.

12. Laifin da Kalu ya aikata abin tir da assha ne, kuma babbar barnace.

Lauyoyin Kalu

Babban lauyan Kalu ya roki kotu ta sassauta masa, saboda ba a taba kama shi da wani laifi a bay aba.

“Kuma akwai dubban ma’aikatan da ke karkashin sa, sannan da shi suka dogara wajen neman abincin su.
“Kuma Kalu na fama da rashin lafiya.

“Don haka muna rokon kotu ta yi la’akari da wadannan bayanai kafin ta yanke masa hukunci.”

Sannan lauya ya ce Kalu ya rike jihar Abia tsawon shekaru takwas tare da yi wa al’ummar jihar aiki tukuru.

“Don haka kada Mai Shari’a ya yi amfani da wannan laifin da ya ce Kalu ya aikata, ya aibata shi.

Mai gabatar Da kara

Mai gabatar da kara, wato lauyan EFCC, Rotimi Jacobs, ya ce duk da ba a taba samun Kalu da aikata wani laifi a baya ba, wannan hukunci da aka yanke masa zai zama ishara ga duk wanda ya ke ganin zai iya wawurar dukiyar al’umma.

Jacobs ya ce duk wanda ya danne hakkin jama’a, komai dadewa, sai an hukunta shi.

Yadda kotu ta Daure Kalu

Da farko an daure Kalu shekaru 5 a tuhuma ta 1, 2, 3, 4, 6, 7, 8, 9, 10 da ta 11; sai kuma wasu daurin shekaru uku a hutuma ta 23, 24, 25, 26, 27, 28, 29, 30, 31, 32, 33; sannan sai wasu shekaru 12 da aka yanke masa a tuhuma ta 34, 35, 36, 37 da 38 da kuma wasu daurin shekaru 5 a tuhuma ta 39.

Sai dai kuma kotu ta ce a lokaci daya za a rika kidaya kwanaki da shekarun kowane dauri. Wato kenan shekaru 12 kadai zai shafe a tsare.

Tuni dai an tafi da su kurkuku. Za a jira a yi yadda za ta kwaranye idan Kalu ya daukaka kara nan gaba.

Share.

game da Author