Dalilin da ya sa Sarkin Bichi ya cire hakimin da ya nada mahaifinsa Ado Bayero a 1963

0

Masarautar Bichi ta tsige hakimai biyar, cikin su kuwa har da Muktar Adnan, wanda shi ne Hamikimin Dambatta, kuma daya daga cikin Masu Nana Sarki a Masarautar Kano.

Dambatta dai na daya daga cikin hakiman da suka zabi Sarkin Kano Ado Bayero, kuma shi ne ya nada masa rawanin farko, cikin 1963.

Sauran wadanda aka tsige din sun hada da Hakimin Tsanyawa, Dawakin Tofa, Minjibir da na Bichi.

Aminu Ado Bayero, sabon Sarkin Bichi ya tsige su, kuma da ne ga Ado Bayero.

An tabbatar da cewa ya cire su ne sakamakon kin yi masa mubayi’a da kuma kin amincewar su da sabbin masarautun da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya nada.

Ya na cikin masu nada sarki a Kano, kuma shi ne ya nada wa Ado Bayero rawani, bayan sun zabe shi kuma an tabbatar da shi a cikin 1963.

Ana zargin wadanda aka cire din da nuna goyon bayan su ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, wanda ake ganin Ganduje ya kirkiro sabbin masarautun ne domin ya raje masa karfin sarauta da kuma karsashin mulki.

A yanzu dai masarauta biyar ce kenan a jihar Kano. Sai dai kuma jama’a da daman a mamakin yadda gwamnatin jihar Kano ke take umarnin kotu, domin kotun ta hana tabbatar da masarautun.

Duk da wannan birki da kotun Kano ta taka, bai hana Masarautar Bichi tsige hakiman guda biyar ba.

Kafin kirkiro wadannan masarautu hudu, wato Bichi, Karaye, Dambatta, Rano Sarkin Kano ne kadai Sarki a Masarautar Kano, tun bayan da na Hadejia, Kazaure, Gumel da Dutse su ka koma karkashin Jihar Jigawa.

KARAYE

Shima Sarkin Karaye ya tsige hakiman Kiru da Rimin Gado.

An cire hakimai biyar daga Masarautar Bichi, kwana biyu bayan cike wasu Hakimai biyu a jihar Masarautar Karaye.

PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda sabuwar Masarautar Karaye ta warware rawanin Hakimin Kiru, Ibrahim Hamza da na Rimin-Gado, Shehu Muhammad, saboda zargin su da rashin biyayya ga sabuwar masarautar.

Majalisar ta yanke wannan sashwarar tsige su ne sakamakon wani zaman da ta yi, a karkashin shugabancin Sarkin Karaye, Ibarahim Abubakar, a fadar sa da ke Karaye.

Wannan sanarwa na kunshe ne a cikin bayanan sa majalisar masarautar ta fitar a karkashin Kakakin Masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa.

“Majalisar Masarautar Karaye na sanar da nadin Alhaji Auwalu Ahmad, a matsayin Hakimin Rimin Gado, Magajin Rafin Karaye a matsayin Hakimin Kiru sai kuma Alhaji Garba Alhaji a matsayin Danmajen Karaye.”

Sannan kuma an amince da nada Shehu Ahmed a matsayin Hakimi Karaye.

Ana ganin cewa dukkan wadannan hakimai da aka tsige, an yi haka ne da daurin gindin Gamna Ganduje.

Share.

game da Author