Da ya daga cikin kannen sanata Kabiru Marafa, Sambo Marafa da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya nada babban mai ba da shawara ya yi murabus daga kujerar.
Marafa ya bayyana cewa yayi haka ne domin ya maida hankali ga harkokin sa na kasuwanci da sauran abubuwan da ya sa a gaba.
” Babu wani abu da ya shiga tsakanina da gwamna Matawalle, Ina so in maida hankali ga wasu harkoki na ne ya sa na ajiye aikin kwamishinan.
Shima kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Bilyaminu Shinkafi ya ajiye aiki. Haka shi ma Jamilu Zannan da aka nada kwamishinan Ilimi bai amshi wannan nadi ba.
Ya koka cewa gwamna Matawalle bai gana da su ba kafin ya sanar da nadin nasu. Kawai ji yayi wai an nada shi.
Jamilu ya kara da cewa bai gamsu da yadda matawalle ke gudanar da mulkin Zamfara ba.
Shi ko Marafa ya yi wa Matawalle fatan Alkhairi sannan ya kara bayyana cewa ya na nan a matsayin wansa har gobe.
Matawalle ya gode wa wadanda suka yi murabus sannan yayi musu fatan alkhairi na nasara ga abinda suka sa a gaba.
Discussion about this post