Kungiyar Ma’aikatan wutan lantarki ta kasa ta bayyana dalilan da ya sa ta yi yajin aikin kwana daya da ya saka duk kasa cikin duhu ranar Laraba zuwa Alhamis.
Shugaban kungiyar Ma’aikatan Joe Ajaero ya bayyana cewa wani abu da ya fi tada musu hankali cikin jerin abubuwan da ya sa suka yi wannan yajin aiki shine kin biyan ma’aikatan da aka kora bayan saida kamfanin wutan lantarki ta kasa, NEPA.
” Tun da aka saida NEPA a 2013 aka kori ma’aikata akalla 2000. Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu ba ace musu komai ba, Mutane suna ta wahala. Mun kai kukan mu hukumar BPE tun a wancan lokaci amma hukumar da ita kanta gwamnati bata ce mana komai akai ba.
” A dalilin haka muka ga abinda ya dace mu yi gwamnati ta saurare mu shine mu ja wa gwamnati kunne da yi mata gargadi ta hanyar fara yajin aiki koda na kwana daya ne kowa ya ji ajika. Kila a karkato a waiwaye mu yanzu.
Bayan haka kuma shugaban ya kara da cewa hatta ma’aikatan da suke aiki a kamfanonin samar da wutan lantar ta kasa ba a biyan su kudaden su yadda ya kamata wato yana nufin albashi.
” A bisa wadannan dalilai yasa dole mu nemo hakkunan mu daga gwamnati ta hanyar yin irin wannan yajin aiki domin tunatar da su game da abinda ya mace su tunda wuri.