Kotun Daukaka Kara da ke Legos, ta daure tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Kalu shekaru 12 a kurkuku.
Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Mohammed Idris ya kama Kalu da laifin zambar kudade naira bilyan 7.65
Ya bada sanarwar daurin ne bayan da ya karanta bayanin kama shi da laifi. Daga nan ya yanke masa daurin shekaru 12 a kurkuku.
Shekaru 12 kenan ana kwatagwangwama da jekala-jekalar wannan shari’a, wadda ta ki ci, ta ki cinyewa.
An gurfanar da Kalu tare da kamfanin sa Slok Nigeria Limited da kuma tsohon Daraktan Harkokin Kudade na Gidan Gwamnatin Jihar Abia, a zamanin mulkin Kalu, mai suna Udeh Udeogu.
KARANTA: KARSHEN TIKA-TIKA: Kotu ta kama Orji Kalu da laifin zambar naira bilyan 7.2
An kwashe shekaru 12 ana cajin sa da laifuka 39, wadanda EFCC ke zargin ya aikata, da suka shafi zambar kudade har naira bilyan 7.65 a tsakanin 1999 zuwa 2007.
EFCC ta zargi Kalu da karkatar da naira bilyan N7,197,871,208.7 zuwa asusun Slok Nigeria Limited, wanda kamfanin sa ne shi da iyalin sa, a bankin Inland Bank Plc da ke Legas.
EFCC ta ce an zabtari kudaden ne daga asusun jihar Abia, aka rika kwasar su da kadan-kadan ana kimshewa a asusun Slok da ke Inland Bank, Apapa, Legas.
Mai gabatar da kara a madadain EFCC, Rotimi Jacobs, ya ce Kalu ya karya doka ta Sashe na 17(c) ta wadda ta haramta harkallar kudade ta shekarar 2004.
Don haka Jacobs ya ce hukunci ya wajaba a kan Kalu, kamar yadda Sashe na 16 na wannan doka ya shar’anta.
Sai dai kuma wadanda ake tuhuma din sun ki amincewa da aikata dukkan laifukan da ake tuhumar su.
Yayin da ake wannan shari’a, mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu 19, yayin da wadanda ake karar suka gabatar da kariya da kan su.