CIN HANCI: An daure ma’aikatan INEC shekaru 42 a kurkuku

0

Babbar Kotun Yola a karkashin Mai Shari’a Nathan Musa, ta yanke hukuncin daurin shekaru 21 ga kowane ma’aikacin Hukumar Zabe su biyu da aka samu da laifin karbar toshiyar bakin naira milyan 362.

Sun karbi kudaden ne daga hannun tsohuwar Ministar Harkokin Man Fetur, Diezani Madueke, a lokacin zaben 2015.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda aka kama da laifin, wato Ibrahim Mohammed da Sahabo Iya-Hamman, Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a kotun.

Har yanzu dai Diezani ta na gudun hijira a kasar Ingila, tun bayan faduwa zaben da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi.

Da ya ke yanke hukunci a yau Alhamis, Mai Shari’a Musa ya bayyana cewa ya yi amfani da shaidu 15 da suka gurfana gaban sa suka bayar da shaida a kotu.

Sannan kuma yanayin amsoshin da wadanda ake zargin suka bayar ga kotu, duk hakan sun tabbatar da cewa tabbas sun karbi kudaden da ake zargi sun karba.

Ya ce su biyun sun karbi naira milyan 362, suka raba kashi 5 bisa 100 na kudin ga wasu jami’an INEC, sauran makudan kudaden kuwa ba a san inda aka yi da su ba.

Ya ce an yi musu sassauci ne saboda lauyan su ya nemi kotu ta yi musu sassauci. Dalili kenan kotu ta daure kowanen su shekaru 7 a kowace tuhuma, daga tuhumomi uku da ake yi wa kowanen su.

Hakan na nufin kowane su ya samu daurin shekaru 21 kenan.

Sai dai kuma babban sassaucin da kotu ta yi musu, shi ne za su yi zaman wa’adin shekaru bakwai-bakwai din a lokaci guda.

Wato maimakon shekaru 21, kowanen su zai shafe shekara bakwai gidan kurkuku kenan.

Daga nan kuma Mai Shari’a ya umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Muhammad Adamu da ya hada kai da ‘yan sandan kasa da kasa domin su cafko Diezani, a gurfanar da ita, domin ita ma a yanke mata na ta hukuncin.

Share.

game da Author