A yau Litinin ne Hukumar Kwallon Kafa ta Turai ta kammala hada kungiyoyin da za su kafsa da juna a zageye na biyu na cin kofin Zakarun Turai, wato Champions League.
Kungiyoyi 16 da suka fito daga share fage ne aka hada a yau, inda kowace ta san wadda za ta kara da ita, a ci gaba da buga gasar siri-daya-kwala da za a fara.
Za a ga yadda Real Madrid za ta karke da Manchester City, ko kuma yadda Napoli za ta iya kwatar kan ta a hannun Barcelona.
Valencia za ta yi kare-jini-biri-jini da Atalanta, kafin a ga wanda zai ga bayan wani. Yayin da Tottenham za ta gwada kwatar kan ta a hannun RB Leipzig, ko kuma Mourinho ya koma gida tun da jijjifin safiya.
Athletico Madrid za ta yi gwagwagwa ita da Liverpool, wadda ita ke rike da kofi a halin yanzu. Ita kuwa Juventus, za ta kece raini da FC Lyon.
Ya rage ga PSG ta kori Brussia Bortmund, matsawar ta na so ta kai ga gazaye na gaba.
GA YADDA ZA SU YI GWAGWAGWA NAN
Manchester City vs Real Madrid
Barcelona FC vs Napoli
Valencia vs Atalanta
RB Leipzig vs Tottenham
Atletico Madrid vs Liverpool
Lyon vs Juventus
Dortmund vs PSG