Buhari ya nada Adamu Shugaban Hukumar AMCON

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya cire Muiz Banire daga shugabancin Hukumar Kula da Kadarorin Najeriya.

Daga cikin aikin AMCON shi ne karbo basussuka daga kamfanonin da suka ci bashin bankuna suka ki biya, ko kuma suka kasa biya.

Sannan kuma ta na da ikon kwace kadarorin kamfanoni ko masana’antun da suka ci bashin da suka ki biya.

Buhari bai bada dalilin tsige Banire daga shugabancin AMCON ba.

Jama’a da daman a mamakin cire shi daga aka yi, domin cikin watan Disamba, 2018 aka nada shi.

Shekarar sa daya kenan kadai da hawa shugabancin hukumar ta AMCON.

An cire Banire mai shekaru 53, kwana daya tal bayan cire Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida ta Kasa, FIRS, Babatunde Fowler, aka nada Muhammadu Nemi.

Buhari ya maye gurbin Banire da Edward Adamu, kuma a yau din ne Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa wasikar neman amincewa da nadin da ya yi wa Edward Adamu.

Ba a san dalilin cire Banire ba, domin wata 12 kadai ya shafe a shugabancin AMCON.

Idan ba a manta ba kuma, jiya ne Babbar Kotun Legas ta umarci AMCON cewa ta gaggauta kwace kadarorin kamfanin Jide Omokore, saboda bashin naira bilyan 29 da ya kasa biya.

Sunan kamfanin Cedar Oil and Gas Exploration and Prpduction Limited.

Share.

game da Author