Bangaren kungiyar Boko Haram ISWAP da suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan kungiyar jinkai ta ‘Action Against Hunger’ sun kashe su.
Kungiyar basu kashe Grace Taku ba da ita ce mace daya cikin wadanda suka yi garkuwa da din.
Ahmed Salkida, fitaccen dan jarida ne ya saka bayanin kisan wadannan ma’aikata a shafinsa ta tiwita.
Idan ba a manta ba kungiyar ta yi garkuwa da wadannan ma’aikata su biyar a wajen aikin agaji ga mutanen da suka tagayyara a dalilin hare-haren Boko Haram.
PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda Boko Haram din suka yi garkuwa da wadannan mutane mutane a wani harin kwantar bauna da suka yi wa motar su a watan Yuli.
Tun a watan Satumba suka kashe mutum daya Saura mutane biyar cikin wadanda suka yi garkuwa da.
Yanzu sun kashe ma’aikata hudu cikin sauran biyar din.
Mace daya kuma da ta rage sun mai da ita baiwa.