Boko Haram sun kashe ma’aikatan Jinkai, sun arce da wasu a Barno

0

Boko Haram sun kashe wasu ma’aikatan jin kai na kungiyar majalisar dinkin duniya, UN a jihar Barno.

An bayyana cewa an kashe wadannan mutane ne a hanyarsu ta zuwa garin Maiduguri daga Mongonu.

” Ina tabbatar muku da cewa Boko Haram sun far wa ma’aikatan Jinkai na UN a hanyarsu ta zuwa garin Maiduguri daga Mongonu. An kashe wasu daga cikin ma’aikatan, sannan sun arce da wasu.

An kashe mutane uku a harin sannan an yi garkuwa da wasu sannan biyu daga cikin wadanda aka kashe, Mata ne.

Kungiyar jinkai mai suna Alima da ke aiki karkashin UN ne ta fada cikin wannan tsautsayi.

Ita dai wannan kungiya, wannan shine karin farko da ta fara aiki a jihar Barno. Saidai duk da kokadin da muka yi domin ji daga bakin kungiyar ya ci tura.

Sannan kuma UN ta ce ba za ta iya ba da bayanai dalla dalla ba game da harin sai ta kammala bincike a kai.

Share.

game da Author