A wani samamen aikin binciken leken asiri da wakilin PREMIUM TIMES ya yi a kamfanin madara na FrieslandCampina da ke garin Iseyin, cikin jihar Oyo, ya ci karo da wasu kananan yara, Yusuf Isah mai shekara shida da kuma Tijjani Abubakar mai shekaru 14.
Tsakanin rugar su da masana’antar tace madara ta FrieslandCampina, tafiyar minti 40 ce.
Dokar Hana Sa Yara Aikin Karfi
A karkashin dokokin Najeriya dai wadannan yara kamata ya yi a ce duk su na makaranata. Haka dokar Majalisar Dinkin Duniya ta Nasarar Muradun Karni da ta Hukumar Kare ‘Yancin Dan’Adam da ma Kungiyar Kare Hakkin Kwadago ta Duniya, duk ba su amince a rika sa kananan yara gudanar da aikin karfi wani ko wasu na cin moriyar wahalar da yaran ke yi ba.
Sai dai kuma da ya ke an sa kafa sanye da takalmin karfe an take wadannan dokoki, shi ya sa wadannan yara a kullum rana tun daga safiya har yammaci ba su zuwa makaranta, sai dai su rika kiwon shanu tare da tatsar madarar da kamfanin FrieslandCampina ke tacewa ta na sayarwa.
Kowace rana, tun daga karfe 5 na asubahi wadannan yara ke tashi su fara bin kowace saniya su na tatsar nonon ta. Can wajen karfe 11 na rana kuma, sai su ja zugar wadannan shanu zuwa cikin jeji domin kiwo.
A wannan kiwon suka kwashi tafayar kilomita da dama, kuma a kullum a kasa, sun a irin wannan tsohon yayin kiwon shanu, wanda sauran kasashen duniya sun daina irin sa, sai fa nan Afrika ta Yamma kawai.
Wadannan kananan yara sai rana ta fadi su ke komawa gida. Za su kwanta kusa da shanun, su na gadin su, a cikin wannan yanayi da ake ciki na fadace-fadacen makiyaya da manoma.
Ba Yusufa da Tijjani ne kadai kananan yaran da ke aiki a wannan gandun dabbobin tatsar madarar da Fulani ke tara wa FrieslandCampina ke tacewa ba. Akwai Mohammed Isah dan shekara 13 da ma sauran wasu kananan yaran masu yawan gaske, da ke irin wannan aiki a Fashola, Maya, Saki, da Alaga, inda FrieslandCampina WAMCO, kamfani mafi girma mallakar Royal FriieslandCampina masu yin Peak Milk da Three Crowns ke samun madara kindirmo.
Ba Makaranta Sai Makarkata
Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce akwai akalla yara kanana milyan 10.5 masu gararamba ba tare da zuwa makaranta ba. Da yawan wadannan yaran kuma na daji su na kiwon shanu, kamar yadda yaran da ke tatsar wa kamfanin FrieslandCampina madara da yi musu kiwon shanu.
Sai dai kuma duk da haka, gwamnatin Najeriya ba ta yin wani abin a zo a gani domin tilasta aiki da wannan doka ta hana sa yara kanana aikin bautar da ake sa su tun karfin su bai kai ba.
Kura da Shan Bugu, Gardi da Kwasar Kudi
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar tare da ziyarar gani da ido da wakilin ta ya kai a cikin rugage kamar 12 a jihar Oyo, ya tabbatar da yadda ake amfani da aikin karfin da ake sa yara kanana ana bunkasa yawan madarar FrieslandCampina.
Binciken mu ya nuna wannan kamfani ya bijire wa bin dokar hana yara yin aikin karfi. Maimakon haka, sai riba kamfanin ke ci da gumin yaran kanana.
Duk da wannan kamfani a jihar Oyo ya ke, amma dai a kullum ya na samun madara kindirmo ne daga wadannan yara masu tatsar masa madara da kiwon shanu.
Sai dai kuma ya na da kyau a gane cewa ba fa kai tsaye kamfanin FrieslandCampina ya dauki yaran aiki ba ne.
A cikin wasu kauyukan dai kamfanin FrieslandCampina ya agaza da famfon ruwa da kuma hasken sola.
Ko a ka’idar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a 2011, ta gindaya sharuddan gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da tauye ’yancin jama’a ba ko danne hakkin kananan yara ta hanyar sa su aikin karfi.
Karya Dokar Najeriya da ta Netherlands
Yadda yara kanana ke aikin karfin samar wa FrieslandCampina madara ya saba wa Dokar Kare Hakkin Kananan Yara ta Najeriya har ma da ta Netherlands. A kasar Netherlands inda can ne tushen FrieslandCampina, babban laifi ne a rika amfani da karfin kananan yara ana samun kudi ta hanyar sa su aikin kwadago.
“Ba ma kasar Netherlands ba ce ta farko saka wannan dokar kare ’yancin kananan yara. Australia da Faransa da Ingila duk sun bi sahu.
Yara Masu Tatsar Madara
Lokacin da wakilin PREMIUM TIMES ya samu Sanusi a garken shanun sa, da ke kauyen Igbokeke a Karamar Hukumar Oyo ta Yamma, cikin watan Oktoba, ya same shi wasu ‘ya’yan sa biyu sun gama tatsar madara kenan.
Cikin yaran kuwa akwai Yunusa mai shekara 10.
“Idan ka na so ka ga yadda ake tatsar madara daga nonon saniya, to ka dawo da sassafe.” Haka Sanusi ya shaida wa wakilin mu.
Ya ce shi asalin sa daga Jihar Neja ya yi hijira zuwa Oyo. Ya ce tilas ya sa dan sa Yunusa aikin tatsar madara.
Ya yi korafin rashin zuwan yaran sa makaranta, ga shi kuma aikin tatsar madarar da yaran ke yi, ba biyan su ake yi ba.
Tun da sassafe sai kamfanin madara ya tura matasa a kan baburan okada, su je rugage su dauko masu madarar da yaran Fulanin suka tatsar musu.
Ana biyan kowane dan acaba naira 80 zuwa naira 100. Ya danganta ga nisan rugar da ya je ya dauko madarar. Cikin masu dauko madarar har da wani mai suna Umar Mohammed da Wakilin mu ya yi hira da shi.
Ya ce ya na dauko wa FrieslandCampina madara daga Olonje da Alaruba, kauyukan da ke cikin Karamar Hukumar Oyo ta Yamma.
Ya ce duk kananan yara ne da ba su ma kai shekara 15 ba ke tatsar madarar.
Kamfanin FrieslandCampina dai ya yi cinikin naira bilyan 123 a cikin 2016, daga cinikin kayan madara da dangogin ta a nan Najeriya. Haka dai rahoton kamfanin na 2016 ya bayyana.
Kenan daga cikin wadannan makudan kudade, akwai kudaden da kananan yara suka yi gumi karcat su na yi wa FrieslandCampina aikin karfi, wanda dokar Najeriya, ta Netherlands, Majalisar Dinkikin Duniya, UNICEF da ILO sun sun haranta.
Cikin 2019 dai akalla kamdfanin ya samu madara kusan lita 789.5 daga jihar Oyo, kamar yadda wasu takardun bayanan da kamfanin ya nuna wa wannan jaridar.
Shi kuwa sakataren kungiyar makiyayan Iseyin, Husseini Tijani, cewa a Iseyin kadai ana samar wa kamfanin madara lita 5,000 a kowace rana.
Ya ce kamfanin na da wurin da ake tattara masa madara a Saki, inda a kullum ake tara masa akalla lita 40,000.
Tijjani ya ce akwai akala da fahimta tsakanin makiyayan yankin da kamfanin FrieslandCampina, saboda su na tara masu madara sosai.
Kamfanin ya kuma tsara makiyayan har ta kai an rika ba su horon yadda za su rika killace madarar da suka tatsar wa FrieslandCampina din.
Inda dai matsalar ta ke, ita ce hanyar da ake bi ana sa kananan yara aikin karfi, maimakon a tallafa musu su yi karatu.
FrieslandCampina ya yi alkawarin yin bincike, yayin da PREMIUM TIMES ta sanar masa abin da ta binciko ke gudana.
Sai dai kuma da farko musantawa suka yi, suka ce babu wani wuri da kamfanin na su ke cin moriyar aikin karfin da kananan yara ke yi.
Sai dai kuma yayin da Kakakin Yada Labaran su mai suna Hamilton ya ga hujjoji kuru-kuru, sai ya ce su na kokarin tsaftace harkar, kuma su na bada horo.
Sannan kuma ya ce za su yi kwararan binckike su gano yadda al’amurran ke gudana.
Ya ce za su ci gaba da yin dukkan iyakar kokarin su domin su ci gaba da inganta tsarin da suke tafiyar da FrieslandCampina a kai.