BAUTA: Rahoton PREMIUM TIMES ya sa kamfanin madara ‘FrieslandCampina’ nada masu binciken musamman daga Birtaniya

0

Katafaren kamfanin nan mallakar ‘yan kasar Netherlands, FrieslandCampina mai yin madara, ya nada kamfanin bincike na Birtaniya mai suna Partner Afrika, domin yin binciken rahoton da PREMIUM TIMES ta fallasa yadda ake saka yara aikin karfi wajen samar da madarar da kamfanin ke sarrafawa Najeriya.

Kamfanin ya ce a shirye ya ke ya kawar da tsarin bautar da kananan yara wajen tara masa dimbin madarar da ya ke sarrafawa.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ne ta fallasa yadda ake sa yara kanana aikin karfin tatsar madara, duk kumwa da cewa dokokin kasa da kasa sun haramta haka.

Kamfanin FrieslandCampina dai shi ke yin madarar Three Crown da Peak Milk da sauran nau’ukan dangogin su a nan Najeriya.

KARANTA: BINCIKE: Yadda kananan yara ke bautar aikin samar da madara wa kamfanin FrieslandCampina

Daya daga cikin daraktocin kamfanin mai suna Ore Fameruwa, ya fitar da sanarwa a ranar Laraba cewa domin tabbatar da abin da ke faruwa da kuma magance shi, FrieslandCampina ya nada kamfanin bincike mai suna Partner Afrika, domin ya binciko sannan a daina wannan tsari na bautar da yara wajen tara wa kamfanin madarar da ya ke sarrafawa, musamman a jihar Oyo.

Akasarin kananan yaran dai duk Fulani ne, kuma ba su zuwa makaranta.

Sannan kuma ya ce za su tabbatar duk yadda za a ci gaba da aikin tattara madarar, ya yi daidai da dokar da Jihar Oyo ta 2006 ta shimfida.

Daga kuma a ranar Laraba, FrieslandCampina ya jinjina wa PREMIUM TIMES dangane da binciken da jaridar ta gudanar, wanda ya ce hakan zai zaburar da su wajen gaggauta yin bincike da kuma magance duk inda matsalar ta ke.

Tuni dai gwamnatin kasar Netherlands wadda da daurin gindin ta da kuma hadin kan ta ne FrieslandCampina ke aikin sarrafa madara a Najeriya, ya bayyana nada masu bincike.

Har zuwa yanzu dai Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnain Jihar Oyo, inda ake bautar da kananan yaran, ba su ce komai ba tukunna.

Share.

game da Author