E! Shekarar 2019 ta zo wa ‘yan Najeriya kamar yadda kowace shekara kan zo ta tafi. Ga shi dai sauran ‘yan kwanaki uku ta wuce mu shiga 2010, amma fa 2019 ta zo da yayume-yayumen tarkacen komatsai da kwarangwatsan diggigar guguwar da ta hargitsa al’amurra da dama a kasar nan.
Akwai abubuwan assha, alheri, sharri, sam-barka, Allah saka da alheri da kuma na Allah-wadai. Wasu sun ci moriyar 2019, wasu kuwa idan muka shiga 2020, to ko kiran sunan 2019 aka yi sai ran su ya ba ci.
2019 ta zo wa wasu a tsaye, wasu a karkace ta zo masu. Akwai wadanda shekarar ta zo masu a baude, assake, waske, tazgade, makance, gurgunce ko dimauce.
2019 dannau ce, ta shigo tun cikin Janairu ta danne wasu, kuma har yau sun kasa tashi. Kuma wannan shekara ba ta da tausayi, domin wadanda 2019 ta halaka ko ta talauta su na da dimbin yawa. Ta bar za ta wuce ta bar wasu a kunce, wasu a takure, wasu a matse, wasu a bankare, wasu a kulle, wasu ma a daburce kuma a wurwurce.
2019 da ta shigo da katon kulkin ta a hannu, wanda ta shafe watanni 12 ta na kwankwatsar ‘yan Najeriya. Ta kwankwatsi kawunan mutane da dama. Ta gwaggwabji hakoran dimbin jama’a.
Wasu sun hadu da azal, wasu kaddara, wasu tuggu kuma algunguman mutane suka ga bayan su. An kori wasu an nada wasu. An tsige wasu an kuma ture wasu.
Gwamnati ta yi aiki kuma ta ki aiki. Manyan jami’an gwamnati da aka tattago aka sa cikin gwamnati, da yawan su sun tafka aika-aika.
Ko ma dai me kenan, 2019 ta fara da kwatagwangwama, kuma a cikin wata kwatagwangwamar za ta wuce nan da ‘yan kwanaki uku.
2019: Shekarar dawurwurar zabe
Wato yaro na goye kadai ba zai manta da zaben 2019 ba, shi ma don hankalin sa bai kai ya san irin kwamacalar magudi, rinto, kwace, fizgen akwatin zabe, kora ko kisa da kone-konen ofisoshin Hukumar INEC da aka yi ba.
Duk wasu dokokin da INEC ta gindaya ta ce kada a karya, babu wanda ba a karya ba. An ga tashin hankali kiri-kiri a yadda zaben gwamnan jihar Kano da na Kogi da Rivers da Bayelsa ya kasance. Kuma duk wanda ke jin labarin ‘inkwamkulisib’, to daga 2019 ya san ta farin-sani, ba sanin-shanu ba.
2019: Shekarar ambaliyar karin kudin haraji
Duk wanda ya kira 2019 shekarar jin-jiki ko shrkarar jiki-magayi, bai yi laifi ba. Gwamnatin APC da ta yi alkawarin kawo sauyi da canji da saukin rayuwa, sai kuma ta koma ta na shigo da haraji iri daban-daban, ta hanypyi daban-daban.
Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi hanyoyin samun kudaden shiga ga gwamnatin tarayya domin gudanar da ayyukan raya kasa da raya al’umma. Sannan kuma domin biyan karin kudaden albashin da gwamnatin tarayya ta yi .
An wayi gari ko kallon gwamnati ka yi, sai ta nemi ka biya ladar kallon da ka yi ma ta. Idan ma ita ce ta kalle ka, sai ka biya ta ladar kallon ka da ta yi.
2019: Shekarar da ruwa ya ci kwarawan asali
Zaben 2019 ya yi mummunar ambaliyar da ta ci wasu manya da mashahuran ‘yan siyasa a Arewa da Kudancin kasar nan. Ruwa ya ci Atiku Abubakar, ya ci Bukola Saraki, Abdul’aziz Yari, Shehu Sani, Dino Melaye, Sanata Hunkuyi, Ambode da ma wasu da dama.
2019: Shekarar fatali da wasu ministoci
Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari zai sake nada ministoci bayan sake lashe zaben 2019, sai ya yi fatali da Abdul-Rahman Dambazzau na Harkokin Cikin Gida da kuma Solomon Dalung na Wasanni, sannan sai Mansir Dan Ali na Harkokin Tsaro da kuma wasu daban.
Cire su ba abin mamaki ba ne, ganin yadda musamman al’amurra suka rika tabarbatewa a kasar nan.
Banda cikin ministoci, Buhari ya cire Shugabannin Hukumomi da dama a cikin 2019. An cire Yusuf Shugaban Hukumar Fanshon Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da Fowler, na Hukumar Tara Kudaden Haraji, watau FIRS.
2019: Shekarar ‘yan bindiga da masu Garkuwa
A da, an san Batulatanin ke cikin surkukin jeji da tsoron duk wani abu da ya danganci wayewa. Tsoron shiga birni ya ke yi, kuma tsoron mota da batur ya ke yi. Duniya juyi-juyi. Sai aka wayi gari Bafulatanin da ke cikin jeji ne ke fitowa rataye da bindiga samfurin AK47, ya tare titi ya na bude wuta su na garkuwa da mutane.
Allah kadai ya san yawan mutanen da aka yi garkuwa da su a cikin 2019 tsakanin jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Neja, Kogi da wasu jihohi da dama.
Katsina, jihar Shugaba Buhari ta fuskanci bala’in masu garkuwa da mutane. Babu wanda ya taba tunanin za a je har cikin Daura a sace surikin Shugaba Buhari.
Duk da cewa an samu sauki ba kamar da ba, sakamakon yarjejeniyar da gwamnatin Zamfara da ta Katsina ta kulla domin ajiye makamai, har yanzu a kauyuka musamnan a Katsina da Zamfata akwai yankuna da lungunan da ake garkuwa da mutane.
A Jihar Kaduna can yankin Birnin Gwwri da Jihar Kogi abin na kara muni. Yayin da garkuwa da mutane ya yi sauki tsakanin Kaduna da Abuja, maharan sun karkata zuwa Jihar Kogi, tsakanin Abuja da Lokoja.
Sai dai a yi kiyasi, amma ba za a iya gane yawan bilyoyin kudaden da aka biya kudin diyyar fansar mutanen da aka yi garkuwa da su a 2019 ba.
2019: Mutanen da suka dama a 2019
A cikin wannan shekara an samu wasu mashahuran mashahuran mutanen da suka dama a rayuwar su. Sai dai wasun su ana ganin cewa kunun salalar tsiya suka dama wa al’umma, ba alheri ba.
Gwamna Yahaya Bello na Kogi, ya kafa tarihin cin zabe ta sigar tashin hankali. An yi mummunan magudi da kashe-kashe, da kone-konen da har wata shugabar matan jam’iyyar PDP aka kona kurmus a Kogi.
Yahaya Bello ya ci zabe karo na biyu, kuma Shugaba Buhari na daga cikin na sahun gaban da suka taya Bello lashe zabe.
Abdullahi Ganduje na Jihar Kano shi ma ya kafa tarihin lashe zabe ta hanyar amfani da karfin ‘yan daba da ‘yan jagaliya, musamman a lokacin zabe cike gibi na yankin unguwar Gama, wato “inconclusive election.”
Sannan kuma Ganduje ya kafa tarihin kirkiro sabbin masarautun Bichi, Karaye, Rano da ya yi, abin da a yanzu ya raba gidan sarautar Kano gida biyar. Kuma ya haifar da rudani a Kano.
Abba Gida-gida. Shi ne dan takarar jam’iyyar PDP na gwamna a Kano. Ya samu garin jinin da babu wanda ya samu kamar sa a Arewa, cikin 2019.
Sauran mutanen da suka kafa tarihi a zp19 sun hada Omoleye Sowore, Gwamna Bello Matawalle, Sambo Dasuki, Deji Adeyanju, Bola Tinubu, gogarman APC wanda ya cika mota biyu manya makil da kudi a ranar jajibirin zaben 2019, amma har yau ba a tuhume shi ba.
Gogarman masu garkuwa a Jihar Taraba, Wadume, shi ma ya kafa mummunan tarihi cikin 2019. Karyar sa ta kare, an kama shi tare da spjojin da ke daure masa gindi. Amma har yanzu ba a san halin da maganar me ciki ba.
2019: Shekarar ‘tashin alkiyamar’ Uzor Kalu, Maina, Yari, Adoke da Dickson
An shafe shekaru 12 ana bugun hisabin tuhumar tsohon gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007. An fara shari’a tun cikin 2007, inda aka zarge shi da karkatar da naira bilyan 7.4. Sai cikin 2019 aka yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai a kurkuku. Tuni Kalu na can a tsare.
Mohammed Adoke, tsohon ministan shari’a na zamanin mulkin Goodluck Jonathan, ya tsere daga Najeriya, tun cikin 2015. Cikin watan Disamba din nan an damke shi a Dubai. Bayan sakin sa, ya dawo Najeriya, inda EFCC suka kama shi tun a filin jirgin sama.
Ana zargin Adoke da hannu a harkallar Malabu Oil, wadda daka-daka ce da ta game duniya kowa ya sani.
Maina ya gama gudun maitar harkallar kudin fansho, amma a karshe kurwar maitar ta kama shi bayan ya sake shigo Najeriya.
Siyasa ta yi wa tsohon gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari da na Bayelsa, Dickson, wadanda dukkan su girman kai ya sa siyasa ta sabule musu zani a kasuwa a cikin 2019.
2019: Shekarar takun-sakar Aisha Buhari da Mamman Daura
Milyoyin jama’a sun yi mamakin yadda dangin Shugaba Buhari suka tare cikin Fadar Shugaban Kasa, alhali a farkon zaben sa cikin 2015, Buhari ya ja kunnen dangi kada su rika yi masa karakaina a fada.
Sai dai kuma Buhari ya yi fatali da wannan ka’ida da kan sa, inda ya rakici dan uwan sa, Mamman Daura da iyalan sa, ya ba su gidan zama kusa da shi.
Hakan kuwa ya jawo takun-saka da tonon silili tsakanin Uwargidan Buhari, Aisha da ‘ya’yan Mamman Daura. Wannan rikici ya sa an rika sukar Buhari cewa ya na da nakasu wajen rikon akalar iyalan sa.
2019: Shekarar da ‘yan soshiyal midiya suka yi wa Buhari ‘amarya’
Har yau an rasa yadda aka yi har aka rika watsa ji-ta-ji-tar wai Buhari zai auri Sadiya Faruq, Ministar Agaji da Inganta Rayuwar Al’umma. Kamar da wasa wannan magana ta zama ruwan dare, ta game kasa baki daya.
Masu yada maganar sun yi gamo da katarin a daidai lokacin kuma Aisha Buhari ba ta Najeriya, tsawon watanni biyu. Magana ta yi tsawo har wasu na watsa cewa yaji Aisha ta yi. Wasu ma suka rika cewa Buhari ya sake ta.
Aisha ta dawo a tsakiyar lokacin da maganganun ke da zafi, kuma abubuwan da suka biyo baya daga nan, sun kara tabbatar da cewa uwargidan ta Shugaban Kasa ta ji ciwo surutan batun auren da aka rika watsawa.
2019: Shekarar sa-toka-sa-katsin karin albashi
Alkawarin karin alnashin da gwamnatin Buhari ta yi wa ma’aikatan gwamnati ya zamar ma ta alakakai, domin an shafe shekarar 2019 cur ana tafka mahawara da sa-toka-sa-katsin batun tsakanin Kungiyar Kwadago ta Kasa da ta Jihohi da kuma daya bangaren ita kan ta gwamnati.
Ma’aikata sun san ido su ka an fara biyan naira 30, 000 a matsayin mafi kankantar albashi, amma hakan bai yiwu ba. Karin albashin da aka furka an yi, ya zama dalilin kara bijiro da haraji iri daban-daban, da sharadin za a yi amfani da kudaden wajen fara biyan sabon tsarin albashi.
2019: Shekarar kashe kaifin wukar Yemi Osinbajo
Bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya karade kakaf jihohin kasar nan ya na tallar shirin raba wa masu karamin karfi ‘yan kudaden jan jari, gwamnatin APC ta yi nasara a zaben 2019.
Sai dai kuma bayan Shugaba Buhari ya nada ministocin sa ba zango na biyu, ya nada Sadiya Faruq matsayin Ministar Harkokin Agaji da Inganta Rayuwar Al’umma. An maida duk wasu shirye-shirye da ke karkashin ofishin Osinbajo zuwa karkashin Minista Sadiya.
2019: Shekarar nada ‘yan-amshin-Shata a Majalisar Tarayya
Nada Sanata Ahmed Lawan Shugabancin Majalisar Dattawa da kuma Femi Gbajabiamila Shugaban Majalisar Tarayya, ya nuna a fili cewa a zubin wannan Majalisa ta 9, gwamnati ba za ta samu tirjiya daga majalisa ba.
Alamomi da dama sun tabbatar da haka, domin shugabannin da kan su sun ce ba a zabe su don yin fada da bangaren gudanar da mulki na gwamnati ba.
2019: Sanata Goje ne babban dankolin da ya ci ribar kasuwar 2019
Yayin da a takaice ta bar baya da kura, kuma ta bar abubuwan yabawa da na jinjina. Sai dai kuma ba za a taba mantawa da kashe sauraren shari’ar Sanata Danjuma Goje ba.
Ana neman sama da naira bilyan 20 a hannun sa, amma daidai lokacin da aka nemi ya janye wa Sanata Ahmed Lawan takarar shuganancin Majalisar Dattawa, sai kotu ta karkare tuhumar da ake yi masa tsawon shekaru kusan goma, aka ce bai ci ko sisi ba.
Watakila ba don haka ba, da yanzu Goje ya na kurkuku a kulle, kamar Orji Uzor Kalu.