Ban taba ganin mai kishin dimokradiyya kamar Buhari ba –Yahaya Bello

0

A daidai lokacin da dimbin jama’a ciki kuma har da kungiyoyin kare dimokradiyya na gida da na waje ke jifar Shugaba Muhammadu Buhari da zargin ya na yi wa dimokradiyya karan-tsare, shi kuwa Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya jaddada cewa bai “taba ganin shugaban kasa mai kishin dimokradiyya, kamar Shugaba Buhari ba.

Bello ya ce saboda tsananin riko da igiyar dimokradiyya da Buhari ya yi, har ma ta kai ya bari jama’ar kasar nan da duniya sun san irin halin takun-sakar da ake yi a cikin gidan sa, tsakanin uwargidan sa da kuma dan uwan sa da hadiman sa.

Haka Bello ya fada bayan Aisha Buhari ta zargi dan uwan Buhari Mamman Daura da yin shisshigin shiga hurumin aikin Shugaban Kasa, har ya na bada umarni.

Ta kuma zargi kakakin yada labarai na Shugaba Buhari, wato Garba Shehu da karbar umarni daga Mamman Daura, ba tare da sanin Buhari ba.

Daga nan kuma Bello ya yi bayani dangane da furucin da aka ruwaito cewa Mashawarcin Buhari a Bangaren Tsaro, Babagana Monguno ne ya yi.

An ruwaito Monguno ya na cewa zaben da aka yi na gwamnan Kogi da Yahaya Bello ya sake yin nasara, ya zo da abubuwan da “hankali da tunani ba za su iya dauka ba.”

“Ni dai ina ji a jiki na cewa baa bin da Monguno ya fada aka ruwaito daidai da abin da ya fadi din ba. Saboda zaben da ya gudana ya samar da sakamakon da jama’a suka zaba da kan su.

“Idan ka ce zaben da aka gudanar a Kogi ya zo da abin da hankali bai taba tunanin samarwa ba, to e haka ne, domin hawa na mulki ma a karon farko ya zo da abin da ba a taba yin tunani ba.

“Saboda babu wani da ya taba tunani wadanda ake kira marasa rinjaye za su iya samar da gwamna, ko kuma na ce babu wanda ya taba tuanin gwamna zai iya fitowa daga wadanda ake kira marasa rinjaye. Kuma har ya yi nasara da rata mai yawa, kamar yadda ya yi a karon farko, kuma ya sake yi a karo na biyu.

“Saboda wannan ne karo na farko da mu ka dakile ruruta zaben kabilanci a jihar Kogi. Wannan ne karo na farko da mu ke doshe inda kudaden shiga ke zurarewa, kuma wannan ne karo na farko da Kogi ke kara samo hanyoyin kudaden shiga. To duk ba a yi tsammanin haka ba.

“Za a ce ya zo da abin mamaki, saboda wannan ne karo na farko da gwamna ya dauke wanda ba dan kabilar sa ba a Kogi ya ba shi mukamin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Tarayya.

“Don haka akwai abubuwan da hankali bai tunanin za su samu ba a Kogi, amma a karkashin wannan gwamnati duk sun tabbata, kuma abubuwa na alheri.

“Saboda haka ni ina ganin wadannan abubuwa ne Monguno ke nufi, amma sai aka yi masa wata fassara daban, maimakon a natsu a fahimce shi.

“Wannan ne karo da farko da gwamna Musulmi ke gida coci a cikin Gidan Gwamnati.

Haka nan kuma bai amince da rahoton da Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) aka bayyana Kogi a matsayin jihar da ta fi kowace cin hanci, rashawa da wawurar dukiya ba.

Sannan a baya naira 200 ce kacal ake tarawa kudin shiga a jihar Kogi. Amma sai gas hi a yanzu mu na tara har naira bilyan daya.

Ya yi bayanan irin ayyukan raya kasa da ya gudanar, tare da bugun kirjin cewa Jihar Kogi ce jihar da ta fi saura samun lambobin yabo a fadin kasar nan.

Share.

game da Author