Babu abinda gwamnan Kwara ya maida hankali akai illa ya ci mana mutunci – Saraki

0

Tsohon gwamnan jihar Kwara, kuma tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa sai fa inda karfin sa ya kare tsakanin sa da gwamnatin jihar Kwara game da ci wa mahaifinsa da ya rasu da iyalansa mutunci a jihar Kwara da suke yi.

Saraki ya gargadi gwamna AbdulRazak Abubakar da ya shiga taitayinsa ya maida hankali wajen samar wa mutanen jihar Kwara ababen more rayuwa kamar yadda yayi a lokacin sa ba ya rika bi da na wa iyalan marigayi Olusola Saraki saran mummuke ba.

Babban abin da ya tada wa Saraki hankali shine yadda gwamnan jihar Kwara ya kwace wani fili mallakar mahaifin sa ya ce za a gina gidajen ma’aikatan asibiti ne.

Gwamnatin Kwara ta ce da karfin tsiya aka ba marigayi Olusola Saraki wannan fili ba tare da anbi yadda ake bada filiye a jihar ba.

” A bisa wannan dalili ne ya sa dole muka kwace wannan fili dake rukunin kebabbun gidajen gwamnati domin maida shi ma’aikata.”

Sai dai kuma Saraki ya karyata wannan batu inda ya ce mahaifinsa bai taba tilasta wa gwamnati ko a abaya ba ta bashi wani abu.

” Ina so in tabbatar muku cewa muna da takardun wadannan filaye wanda mahaifin mu ya mallaka. Domin tun a 1980 ya samu wannan fili amma yanzu katsam gwamnati zata bijiro da wani abu da ba haka ba don nuna kiyayya ga marigayi Saraki da Iyalansa. Ba za mu yadda da haka ba.

” Zan kai kara kotu kuma gwamnati ta sani sai fa inda karfina ya kare a wannan fadar domin haka kawai ba zan zuba ido ina gani wasu su zo su yi mana kwace da karfin gwamnati ba don mai asalin wurin ya riga mu gidan gaskiya. Amma ay mu magada muna raye kuma zamu bi hakkin mu.

Share.

game da Author