Ba na da-na-sanin kai aikin gina Jami’ar Sufuri a Daura –Amaechi

0

Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa shi ba shi da wani da-na-sani dangane da kai Jami’ar Sufuri a Daura.

Amaechi ya yi wannan kalamin ne a lokacin da ake gagarimin kaddamar da aikin gina jami’ar, a Daura, Jihar Katsina, a yau Litinin.

“Lokacin da muka kai aikin gina masana’anta a Kajola, ai babu wanda ya yi magana ko surutai, kuma babu wanda ya zage mu. Ba kamar lokacin da yanzu muka kawo aikin gina jami’ar harkokin sufuri a Daura ba.

“Daura dai ai a cikin Najeriya ce, ba a wata kasa can cikin duniya garin Daura ya ke ba. Ba a cikin Jamhuriyar Nijar Daura ya ke ba, ko Mali. To ina laifi ko ainin kafa Jami’ar Sufuri a Daura?

“To ni dai ban a da-na-sanin kawo aikin kafa Jami’ar Harkokin Sufuri a Daura. Kuma ban kawo ta Daura ba don na amfana da wani abu ni a kashin kai na.

Daura dai can ne garin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda dalili kenan jama’a da dama ke korafi kan gina jami’ar a Daura.

Ya ce ilmi na da muhimmanci, kuma kula da cibiyoyin ilmi shi ma abu ne mai muhimmanci. Don haka ya tabbatar kafa jami’ar a Daura za ta samu kula sosai, ba za a bari ta samu wata tawaya ba.

“Da farko kamfanin da zai yi aikin gina Jami’ar kin yarda ya yi ya gina ta a Daura, har sai da na ki sa hannun kwangilar da muka ba su ta aikin gina titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan, sannan suka amince.

“Na ce musu ba fa zan sa hannu a kan aikin gina hanyar jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan ba, har sai kun amince da wadannan sharudda uku.

“Na farko na ce musu sai sun amince za su dauki yaran kasar nan su kai su Chana domin samun digiri a kan aikin fasahar gina titin jirgin kasa.

“To a yanzu haka an tura 60, kuma wannan makon za a kara tura wasu 90, domin su zama 150 cif-cif.

“Abu na biyu shi ne dole su kafa masana’antar hada tarragon jiragen kasa a Kajola, wanda sun amince, kuma yanzku haka ana kan aikin gina masana’antar.

“Ka’ida ta uku ita ce su gina Jami’ar Fasahar Sufuri a Jihar Katsina, a Daura, kuma ga shi zan duk CCECC ya amince zai gina. Don haka mu na godiya ga kamfanin CCECC da kuma gwamnatin kasar Chana.
Amachi ya gode wa Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari da ya bayar da katafaren filin da za a gina jami’ar.

Shugaban Hukumar Kula da Jiragen Kasa, Ibrahim Hassan, y ace wannan jami’a irin ta ce ta farko, kuma za ta bunkasa ilmi da tattalin arzikin kasar nan.

Share.

game da Author