Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa ta na fama da babban kalubalen gurfanar da masu karya dokokin zabe.
Shugaban INEC ne da kan sa, Mahmood Yakubu ya bayyana haka, a taron da ya yi da daukacin Kwamishinonin Zabe na Kasa (RECs), a Abuja.
Yakubu ya ce, yayin da aka dora wa INEC nauyin gurfanar da masu karya dokokin zabe, a gefe daya kuma ba ta da karfin iya kama wadanda ake zargin ballantana gudanar da bincike a kan su.
“Idan babu wadannan kuwa, to babu yadda za a yi a iya yin nasara wajen gurfanar da wadanda suka karya dokokin zabuka.
“Shekaru da yawa mu na aiki ne kafada-da-kafada tare da jami’an ‘yan sanda. Tun cikin 2015, mu na da fayil-fayil na shari’u 149, ciki har da guda 16 daga zaben 2019.” Inji Yakubu.
“Ana gudanar da wadannan tuhume-tuhume ne a jihohi daban-daban inda ake zargin wanda aka gurfanar din ya aikata laifin da ake tuhumar sa.
“Ba kamar shari’un kafin zabe da bayan zabe ba, babu wasu lokuta ko wa’adin da aka gindaya na kammala shari’ar wadanda suka karya dokokin zabe. Shari’a daya za ta iya daukar shekaru da dama ana gaban kotu.
“Wasu shari’un kotu kan yi watsi da su saboda rashin sahihiyar hanyar gurfanar da wadanda ake zargi. A wasu jihohin kuma sai Kwamishinan Shari’ar Jihar, wato Antoni Janar ya shigar da sanarwar ba-kare-bin-damo (nolle prosequi) a kotu. Shi kuma mai shari’a, sai ya kori karar kawai, sai a saki wadanda aka kama da laifin karya dokokin zabe.
“Ko a Kano ma inda aka gurfanar da mutane 40 sakamakon karya dokokin zabe a shekarar 2016, babu wanda zai iya cewa ga yawan wadanda aka daure. Domin zabin dauri ko biyan tara aka ba su. A irin wannan kuwa, su masu daukar nauyin su karya dokar zabe, su za su biya kudin a kotu, sai mai shari’a ya sa a sake su.
“Dalili kenan mu ka hakkake cewa idan aka kafa Kotun Hukunta Masu Karya Dokokin Zabe, za ta taka muhimmiyar rawa wajen gaggauta yanke hukunci kan masu laifi. Musamman idan aka yi la’akari da irin yadda wannan kotu ke hukunta masu magudin zabe a Afrika ta Kudu.”
Daga nan sai ya yi fatan cewa jami’an tsaro za su tashi haikan wajen dakile dukkan masu karya dokokin zabe, tare da gurfanar da masu cin zarafin jami’an zabe da masu jefa kuri’a, tare kuma da damke masu daukar nauyin su.
Yakubu ya nuna damuwa kan irin yadda zabe musamman na gwamna ya zama ko-a-ci-ko-a-mutu.
Ya ce hargitsin da ake yi ya yi muni kwarai, ta yadda magance matsalar kawai ita ce a samo hanyar gaggauta duk wani mai laifi, duk girman sa, ba tare da nuna son rai ba.
Farfesa Yakubu ya ce tsari da fata da kuma shirin da INEC ke wa kowane zabe, shi ne a gudanar da shi cikin nasara, tare da amincewa da abin da jama’a suka zabar wa kan su a ranar zabe.
Discussion about this post