An rufe gidan ‘Mayu’ a Kano

0

Babban sakataren hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu na jihar Kano, Usman Aliyu ya bayyana cewa hukumar ta rufe wani gida da ake kira gidan ‘Mayu’ da mallakin wani mutum mai suna Yahaya Aliyu.

Yahaya Aliyu da aka fi sani da ( Ciroman Sarkin Mayu) ne mai mallakin wannan gidan matsafa dake Makoli, karamar hukumar Dawakin Kudu.

Usman ya ce bayan sun kai wa wannan gida farmaki, sun tadda mutane da dama suna kwance rashe-rashe basu da lafiya. Wasu na neman ayi musu aiki ne ma ajiki amma wai suna wannan gidan mayu.

” Tuni muka kwashe su muka kai inda za a duba su sannan shi kuma muka danka shi ga hukuma.

An rufe wannan gida ne Makoli, karamar Hukumar Dawakin Kudu.

Share.

game da Author