Gwamnatin jihar Neja da handin guiwar kungiyar ‘Society for Family Health (SFH) da sauran kungiyoyin bada tallafi sun raba wa mutane miliyan 6.7 gidajen sauro a jihar Neja.
Shugaban shirye-shirye na kungiyar Christopher Dangana ya sanar da haka wa manema labarai a garin Lafiya.
Dangana yace an raba wadannan gidajen sauro ne a kananan hukumomi 25 dake jihar sannan an kashe Naira biliyan 3 wajen siyan su da ayyukan rabasu.
Ya ce sai da aka raba wa mutane katin karban gidajen sauro miliyan 3,590,605 sannan aka fa raba gidajen kyauta a jihar.
Gwamnati ta yi haka ne domin dakile yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a jihar.
A watan Agustan 2019, Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa lallai sai fa kasashen duniya sun maida hanakali matuka wajen zakulo sabbin hanyoyi da matakan dakile ci gaba da yaduwar zazzabin cizon sairo da ake fama dashi a duniya, in ba haka ba kuwa ba za a kai ga ci ba.
WHO ta ce za a samu nasara a haka ne idan aka kara yawan kudaden da bangaren bincike ke samu a duniya.
A yanzu haka sashen gudanar da bincike na samun kasa da kashi daya bisa dari da haka ya yi kasa da adadin yawan kudaden da ake bukata domin gudanar da bincike.
Shugaban WHO Tedro Ghebreyesus ya yi bayyanin cewa matakan hana yaduwar cutar da ake amfani da su a yanzu haka a duniya tuni sun zama tsoffin hanyoyi.
Ghebreyesus yace lokaci ya yi da WHO tare da hadin gwiwar kungiyoyin bada tallafi za su hadu domin kawo kashen wannan matsala a duniya.
Discussion about this post