An gano cutar ‘Monkey Pox’ a jikin wani dan Najeriya a kasar Ingila – NCDC

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa wani dan Najeriya dake zama a kasar Ingila ya kamu da cutar ‘Monkey Pox’.

An gano cutar a jikin wannan mutumi ne a kasar Ingila bayan ya dawo daga Najeriya.

NCDC ta ce za ta hada hannu da hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar Ingila (PHE) da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) domin dakike yaduwar cutar.

Hukumar ta kuma ce sakamakon binciken da cibiyar gwajin hukumar dake Abuja ta yi ta gano cutar a jikin wasu mutane biyu.

Hukumar ta ce ga dukan alamu cutar ba zai yadu ba a kasar Ingila amma duk da haka za ta dauki matakan hana yaduwar cutar.

Monkey pox cuta ce da ta fara bullowa a Najeriya a 1978 inda daga wannan lokaci cutar bai sake bullowa ba sai a 2017 a jihar Bayelsa.

A wannan lokaci NCDC ta gwada jinin mutane 101 a kasan inda aka samu tabbacin mutane 43 dake dauke da cutar sannan mutane biyu daga cikinsu sun mutu.

Rahotanni sun nuna cewa namun daji kamar su birai da beraye dake shawagi agidajen mutane na daga cikin ababen dake kawo cutar ‘Monkey Pox’.

Sannan zazzabi, yawan jin gajiya a jiki, ciwon jiki musamman baya, kumburin jiki musamman idan cutar ta fara nunawa, fitowan kuraje a jikin mai dauke da cutar na daga cikin alamun cutar.

Guje wa cin naman dabbobin daji kamar su biri, burgu da bera, hana dabbobi yawo musamman wadanda ke kiwon su domin kada su fita su dauko cutar daga jikin dabbobin da suke dauke da cutar kuma a killace dabbobin da suka kamu da cutar saboda hana yaduwar ta da tsaftace muhalli na cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Share.

game da Author