Jami’an tsaro a Jihar Ogun sun damke wani mutum mai suna Taofeek Oyeyemi, wanda ya dirka wa karamar ’yar sa mai shekaru 16 cikin-shege, sannan kuma ya yi kokarin zubar mata da cikin a wajen wani gargajigan likita.
Kakakin ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi ta tabbatar da wannan labari a yau Alhamis, a cikin wata takarda da ta fitar ga manema labarai, a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
An kama wanda ake zargin bayan da mahaifiyar yarinyar ta kai rahoton sa a ofishin ‘yan sanda da ke Ewekoro, cewa mijin ta ya dirka wa ‘yar su ciki, kuma ya yi kokarin zubar da cikin wajen wani likitan da ba shi da lasisin shaidar aikin likita.
Jami’an tsaro sun ce tun da aka zubar wa yarinyar ciki ta ke ta zubar da jini. Wannan ne ya sa aka kamo mahaifin na ta.
Wanda ake zargin dai an tabbatar ya na da ‘ya’ya 17 daga mata daban-daban.
Ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya sha yin lalata da ‘yar ta sa, kuma don ya rufa wa kan sa asiri ne ya kai ‘yar wajen likitan bogi aka zubar ma ta da cikin.
Bincike ya nuna cewa mahaifiyar yarinyar ta rabu da mahaifin tun shekaru da suka gabata, kuma a hannun ta ‘yar ke zaune, har sai watanni shida da ya kwato ta a hannun ta da karfin tsiya.
“Ya ki barin mahaifiyar yarinya ta rike ta. Har sai da wata rana ta zo ganin ta, sai ta same ta cikin jini, sakamakon zubar ma ta da cika da aka yi.” Haka sanarwar ‘yan sanda ta tabbatar.
Ana ci gaba da binciken sa, kuma za a maka shi kotu, domin ya girbi abin da ya shuka.