An damke dan Najeriya da kwayar naira bilyan 2.6 a Indiya

0

Jami’an tsaron Indiya sun damke wani dan Najeriya tare da wasu Indiyawa biyu dangane da zaegin su da ake yi da hannun a safarar kwayar naira bilyan 2.6.

Jami’an tsaro sun ce an damke mutanen uku a birnin Delhi.

Wani rahoto da jaridar Times ta Indiya ta wallafa jiya Talata, ta bayyana sunan dan Najeriya din Chris Jole, sai kuma sauran Indiyawa biyu, Anubhav Dushad mai shekaru 35 da kuma Renuka mai shekaru 27.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sandan birnin Delhi, PS Kushwah ya ce jami’ai sun damke su a ranar 15 Ga Disamba, bayan da suka samu labarin cewa Dushad zai kai wa Renuka wasu daurin dilolin kwayar heroin a kusa da Sabuwar Tashar Jiragen Kasa ta Delhi, da karfe 7 daidai na safiya.

Kushwah ya bayyana cewa an kama su da kwaya mai nauyin KG 12, wadda kudin ta kasuwar ‘yan hada-hadar kwaya ta duniya zai kai naira bilyan 2.6.

Da aka matsa wa Dushad da bincike, sai ya ce ya samu kwayar ne daga hannun wani dan Najeriya mai suna Chris Jole, da ke zaune a unguwar Shiv Vihar a Delhi.

Nan da nan jami’an tsaro suka garzaya suka yi cacukui da Jole, aka yi awon gaba da shi.

Jole ya shaida wa jami’an tsaro wani dan uwan sa dan Najeriya ne mai suna Peter ke kawo masa kwayar, wanda shi ma da kasar Afghanistan ya ce ake turo masa ita.

Jole ya kara shaida wa jami’an tsaro cewa baya ga rarraba kwaya da ya ke yi a ko’ina cikin kasar Indiya, shi da sauran abokan harkar sa kuma na aikawa da kwayoyi a kasashe irin su France, Italy, Canada, UK da UAE.

Ya ce ta kamfanonin aikawa da sakonnin kar-ta-kwana, wato ‘couriers’ suke aikawa da kwayar gari gari, ko kasa-kasa.

Share.

game da Author