An cika shekaru 40 kenan da rabuwa da cutar kyanda ‘Small Pox’ a duniya

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa duniya ta cika shekaru 40 cif kenan da rabuwa da cutar kyanda ‘Small Pox’

Shugaban kungiyar WHO,Tedros Ghebreyesus
ya bayyana cewa an samu nasarar kau da cutar ne a dalilin dunkulewa wuri daya duk kasashen duniya domin fafutikar cutar tun a baya.

“ Duka kasashen duniya sun hadu wuri daya domin ganin an kau da cutar, kuma cikin ikon Allah aka samu wannan nasara gaba daya.

Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da a hadu sannan arika maida hankali wajen yi wa mutane rigakafin cututtuka musamman cututtukan da rigakafi zai iya kauda su.

Bayanan ma’aikatan kiwon lafiya sun nuna cewa kwayoyin ‘Virus’ ne ke haddasa wannan cuta.

Likitoci sun ce kwayoyin cutar na daukar tsawon kwanaki 17 kafin ya nuna alamunsa a jikin mutum.

Alamun cutar sun hada da zazzabi,fesowar kurarraji,amai,ciwon kili da sauran su.

Sun kuma ce babu maganin wannan cuta amma yin allurar rigakafin cutar kafin a kamu da ita na cikin hanyoyin gujewa kamuwa da cutar.

A dalilin haka duniya gaba daya ta daura damara wajen ganin mutane sun yi allurar rigakafin cutar.

Share.

game da Author