Amurka, Ingila da Tarayyar Turai su daina shiga sabgar Najeriya – Fadar Shugaban Kasa

0

Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, ya gargadi Amurka, Ingila da Kungiyar Tarayyar Turai su daina shiga sha’anin Najeriya, musamman idan ana maganar zargin take hakkin dan Adam.

Femi Adesina ne ya yi wannan gargadin jiya Laraba, yayin da ya ke maida martani ga wani rahoto da Turai, Ingila da Amurka suka fitar a kan Najeriya, wanda bai yi wa Gwamnatin Buhari dadi ba.

Kasashen sun bayyana cewa Najeriya a sahun gaba na kasashen da suka yi kaurin suna wajen take hakkin jama’a.

Adesina ya yi wannan bayani ne a lokacin da ake hira da shi a wabi shiri da Gidan Talbijin na Channels TV ke gabatarwa a kowace safiya, mai suna “Siyasa A Yau.”

Adesina ya ce ai Najeriya kasa ce mai ‘yancin kan ta, kamar kowace kasa. Don haka ba ta damu da wani rahoton aibatawa daga wata kasa ko gungun kasashe ba.

Da ya ke magana a kan shigar burtu da kutsen da jami’an SSS suka yi a cikin kotu, suka damke Mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, sai Adesina ya ce, “Najeriya cikakkiyar kasa ce kamar kowace kasa. Don haka ba ta karbar umarni ko hani daga kowace Amurka, Birtaniya ko Tarayyar Turai.

“Mu fa Najeriya ce, kuma ita ma kasa ce kamar kowa. Wadannan kasashen da ake magana kowace na da irin ta ta matsalar. Don haka su je can su ji da abin da su ma ya ishe su. Su bar Najeriya ita ma ta magance na ta matsalolin. Saboda mu fa ba a karkashin su mu ke ba.” Inji Femi Adesina.”

Na Fi Ganin Darajar Ra’ayin Soyinka Fiye da na Amurka, Ingila da Turai

Adesina wanda ya taba rike shugabancin Kungiyar Editocin Najeriya har sau biyu, ya nanata cewa shi har ma ya fi ganin daraja da kimar ra’ayin Wole Soyinka fiye da wasu kasashen waje ko wasu ‘yan kasashen waje masu yin sharhi a kan Najeriya.

“Mu na ganin kimar Farfesa Soyinka. Ba mu da irin sa da yawa a Najeriya ko ma a Afrika baki daya. Amma ra’ayin sa wannan ra’ayin sa ne shi kadai. Idan akwai abin da za a iya dauka daga ciki a yi amfani da shi, sai a dauka a yi amfanin da shi.”

Wasu ‘yan majalisa daga Birtaniya da Amurka sun yi ta kiran a saki Sowore, amma gwamnatin tarayya ta yi kunnen-uwar-shegu da wannan kiraye-kirayen na su.

Baya ga Sowore, wasu daga cikin wadanda gwamnatin Najeriya ta tsare sun hada da tsohon Mashawarcin Goodluck Jonathan a kan Harkokin Tsaro, Sambo Dasuki da kuma Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa Zeenat, da dukkan ukun ke tsare tun cikin 2015.

Share.

game da Author