A taron kungiyar matan gwamnoni da aka yi a Abuja cikin wannan mako uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta nada mai dakin mataimakin shugaban kasa Dolapo Osinbajo a matsayin wacce za ta jagoranci kwamitin yaki da cutar tarin fuka.
Babban sakataren Kungiyar Yaki da Tarin Fuka ‘Stop TB Partnership Nigeria’ Mayowa Joel ya sanar da haka a taron kungiyar da aka yi a Abuja.
Tarin fuka cutace da ake kamuwa da ita ta hanyar shakar kwayar cutar.
Aisha ta ce a dalilin haka take kira ga kungiyar matan gwamnoni da su hada hannu da masu ruwa da tsaki domin dakile yaduwar cutar a Najeriya.
“ Matan gwamnoni na da mahimmiyar rawa da za su taka wajen ganin mutanen Najeriya sun yi bankwana da wannan cuta.
Idan ba a manta ba sakamakon binciken da hukumar WHO da UNICEF suka yi ya nuna cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen duniya 14 da cutar ta yi wa katutu.
Binciken ya kuma nuna cewa a duk shekara mutane 407,000 na kamuwa da wannan cuta a Najeriya.
Sannan daga cikin su kashe 25 bisa 100 ne ke samun maganin cutar.
Najeriya ta fada cikin wannan matsala ne a dalilin rashin gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, rashin samar da isassun magani,rashin kwararrun ma’aikata,rashin kayan aiki da sauransu.
Sai dai kuma gwamnati mai mulki ta maida hankali matuka wajen samar da kayan aiki da gyara asibitocin kasar nan da hakan zai rage matsalolin da ake fama da su.
Discussion about this post