Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta caccaki masu taimaka wa Buhari kan harkar yada labarai da hulda da jama’a cewa wai basu kare mijin ta daga hauragiyar Soshiyal Midiya.
Aisha ta caccaki ministan sadarwa, Ibrahim Pantami, inda ta ce babu abin da yake yi sai cika baki amma yaki ya dakatar da yadda mutane ke caccakar mijinta a kafafen yada labarai.
” A dalilin sakacin Pantami da masu taimakawa Buhari a harkar yada labarai, sai kaga an shiga shafunan yanar gizo ana da caccakar Buhari amma ba za su iya cewa komai akai ba. Shi kansa Pantami da shine ministan sadarwa bai komai akai ba.
” Babu yadda za a samu ci gaba a kasa idan kowa zai fito ya yabo magana yadda yake so akan shugaban kasa kuma a yi shiru ba a hukunta shi ba. Amma idan wani abinda bai taka kara ya karya bane, ko kuma ma baishafe su ba sai ayi ta yada shi ana ta maida martani, amma sukar Buhari bai zama wani abu.
” Nan nan bayan zaben Bayelsa, PDP suka fito suka soki tsohon shugaban kasa cewa suna zarginsa da yi wa APC aiki. Kwatsam sai Fadar shugaban kasa ta fito ta maida wa PDP martani. Ina ruwan ta da PDP. Ai bai kamata ta ce komai ba. Sun kyale Buhari ana caccakar sa yadda aka dama a soshiyal midiya.
” Sannan kuma duk a haka ne aka rika fitowa ana ta yada karerayin wai Buhari zai yi aure. Kuma ba a kama masu yada wannan karerayi ba.
Aisha Buhari ta yi wannan maganganu ne a hira da ta yi da gidan Talabijin din TVC.
Aisha ta na bayanine da nuna goyon bayanta ga kudirin neman a kafa dokar yi wa rubuce-rubuce a yanar gizo wato soshiyal midiya iyaka da hukunta duk wanda ya yi rubutun batanci ga wani.
‘ Yan Najeriya da dama sun yi tir da wannan shiri na gwamnatin Buhari inda suka rika cewa ana so ati haka ne don aci zarafin ‘yan Najeriya da damar da domar kasa ta basu.