ADAMAWA: Yadda rudanin siyasa ya hana gwamnatin mahaifi na tabuka abin kirki -Abdul’aziz Nyako

0

Tsohon dan takarar gwamna kuma tsohon sanatan Adamawa ta Tsakiya, Abdul Aziz Nyako, ya bayyana cewa turnukin harmagazar siyasa ce ta hana mahaifin sa, tsohon Gwamnan Adamawa, tabuka ayyukan inganta rayuwar jama’ar jihar Adamawa.

Abdul’Aziz ya ce dalili kenan jihar Adamawa ba ta amfana sosai da ayyukan raya kasa a jihar.

Nyako, dan Murtala Nyako, ya yi wannan furuci ne a lokacin da Gidan Radiyon Jihar Adamawa ke hira da shi.

An tattauna da shi a karkashin wani shiri mai suna Ribar Dimokradiyya, wanda ake gabataarwa da harshen Hausa.

Ya ci gaba da nuna damuwa cewa kudaden da gwamnati ta rika kashewa a lokacin gwamnatin mahaifin sa domin shawo rikicin siyasa, sun isa a gudanar da muhimman ayyukan da jihar Adamawa za ta zama kasaikacciyar jiha.

“Rikita-riktar siyasar Adamawa ta haifar wa mulkin mahaifina na tsawon shekaru bakwai cikas matuka.

” Fintiri shi ma ya hau mulki a wancan lokacin cikin kwatagwangwamar siyasa. Bala Ngilari ya hau mulki, amma fa ya ci kwakwa sosai. Haka Bindow ya hau ya yi ta fama da kwamacalar siyasa.”

Nyako ya kara yin nuni da cewa jihar Adamawa da Anambra ne jihohin da tsugudidin siyasa ya hana ci gaba.Ya kara da cewa a wadannan jihohin a cikin kowace sa’a ko minti daya, babu wani batu sai na siyasa kawai.

Ya kara jaddada cewa saboda ya na so a yayyafa wa wutar siyasar Adamawa ruwa, shi ya sa da Fintiri ya lashe zaben gwamna ya je ya yi masa murna, tare da alkawarin tafiya tare wajen ba shi shawarwari.

Share.

game da Author