Babbar kotu dake Yola jihar Adamawa ta yanke wa wani baragurbin likita mai suna Ibrahim Mustapha hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru 54.
Alkalin kotun Nathan Musa ya yanke wannan hukunci ne bayan Mustapha ya amsa laiffukan da ake tuhumarsa dashi sannan da neman sassauci daga kotun da ya yi.
Musa yace akan laifi daya zuwa uku kotu ta yanke wa Mustapha hukuncin zama a kurkuku na tsawon watanni shida-shida ko kuma ya biya tarar naira 20,000 akan kowani laifi.
Bisa ga laifi na takwas kotu ta yanke wa likitan hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru uku ko kuma ya biya taran Naira 50,000.
Akan laiffuka na hudu, biyar, shida, bakwai zuwa goma Mustapha zai yi zaman gidan yari na tsawon shekaru 50 kuma babu biyan tara.
Sai dai kuma a dalilin neman sassauci da lauyan Mustapha yayi kotu ta ce mustapaha zai yi zaman gidan Kaso ne na tsawon shekaru 10 da suran ayyuka da zai rika yi da zai biyo baya.
Hukumar jami’an tsaro na SSS ne suka kam Mustapha a watan Yuni 2019 da laifin kula da marasa lafiya batare da lasisi ba.
An zargi Mustapha da laifukan kisa da cutar da kiwon lafiyar mutane da dama a jihar.
Sai dai Mustapha a lokacin ya bayyana cewa tun da ya fara aikin likita yake yi wa mutane fida kuma hakan bai taba yin ajalin wani ba.