Wasu gungun ‘yan takife sun kai hari kan masu zanga-zangar nuna rashin jin dadin yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke take masu rajin kare dimokradiyya da kuma kin bin umarnin kotu.
Daga cikin wadanda aka raunata har da dan gaba-dai-gaba-dai din rajin kare dimokradiyya, Deji Adeyanju, wanda a yanzu haka an kwantar da shi asibiti, sakamakon raunukan da aka ji masa.
Ganau ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu goyon bayan gwamnatin Buhari ne suka kai wa masu zanga-zanga harin.
Wani dan rahoto da ke aiki da gidan talbijin na Arise TV, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa magoya bayan gwamnatin Buhari sun yi wa Adeyanju rubdugu shi da wasu masu masu zanga-zanga, kuma suka fatattake su.
Wani bidiyo da aka watsa a shafukan twitter ya nuna magoya bayan Buhari su na rera wakokin goyon bayan shugaban, sannan kuma su na nausawa wurin taron zanga-zangar, a wajen harabar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam.
Wani ma’aikacin AIT da ya fara watsa bidiyon, a bayyana dauko bidiyon wurin kafin a hautsine, a yau Litinin da safe.
Masu zanga-zangar sun fito ne yau Litinin da safe, bayan cikar wa’adin makonni biyu da suka bayar cewa Buhari ya rika bin umarnin kotu, ciki kuwa har da neman a saki Omoyele Sowore, da ake tsare da shi tun cikin watan Agusta.
A Legas, tsohon babban birnin jihar Lagos ma an yi wannan makamanciyar zanga-zangar, amma jama’a ba su halarta sosai ba.
Discussion about this post