Abubuwa 7 dake kawo kaikayin kai da yadda za a kiyaye

0

Kaikayin kai matsala ce da ake yawan fama da shi sannan da dama a cikin mutane basu san dalilin da ya sa hakan ke faruwa ba.

Wasu likitoci da suka kware a kula da lafiyar farce, gashi da fata dake Harvard a kasar Amurka sun ce mafiyawan lokutta rashin tsaftace jiki musamman kai ne ke haddasa kaikaiyi a kai.

Sun ce a dalilin haka ya zama dole a wayar wa mutane game da haka domin kare su daga kamuwa da wannan matsala.

Ga dalilai guda bakwai.

1. Kwar-kwata

Likitocin sun ce ba sai dole an ga kwaron kwarkwata na yawo a kan mutum bane sannan ake cewa mutum na da kwar-kwata akansa domin kwan kwarkwata na sa a kaikayi a kai shima.

Bincike ya nuna cewa mutane da dama kan samu kwan kwar-kwata a kan su batare da sun sani ba.

Tsaftace kai da ya hada da wanke kai da yin kitso ga mata sannan da aski ga maza na daga cikin hanyoyin rabuwa da kwan kwar-kwata a ka.

2. Amosanin kai

Rashin tsaftace kai, rashin shafa mai a kai, cutar kanjamau da yawan aron matsefi na da ga cikin hanyoyin da ake kamuwa da amosanin kai.

Likitocin sun ce rashin kiyaye wa davwarkewa da wuri na haddasa cutar amosanin ido.

Yawan shafa mai a kai da tsaftace kai zai taimaka wajen rabuwa da amosani.

3. Yawan rufe kai

Likitocin sun ce kan mutum zai yi gumi idan ana yawan rufe shi kuma yin haka na daga cikin hanyoyin dake sa kan mutum ya rika yin wari kamuwa da cuta.

A dalilin haka ake kira ga mutane musamman mata da a daina yawan rufe kai domin guje wa haka. Ha rika bude shi ko da a gida ne domin shan iska.

4. Furfura

Shima furfura ya ba sa a rika yawaita susa kai a ko da yaushe.

Za a iya amfani da lalle domin rage kaikayin sannan shi lalle na rage yawan zubar gashi da kara tsawon sa.

5. Yawan zuban gashi

Rashin Kula da tsufa na sa zunban gashi matuka sannan da cututtuka kamar rashin jini a jiki, rashin wasu sinadarin inganta garkuwan jiki da matsalolin da akan samu a dalilin shan magani.

Likitoci sun ce haka na daga cikin dalilan dake sa kan mutum ya rika yawan kaikayi.

Shafa mai, yin kitso, cin fiya, karas da ganyen da ake ci zai taimaka wajen hana yawan zubar gashi.

6. Makenkero

Kamar yadda ake kamuwa da kwar-kwata a dalilin rashin tsaftace jiki da kai haka ake iya kamuwa da makenkero.

Makenkero na fitowa a kowani bangaren jikin mutum sannan yana sa yawan zubar gashi idan ya fito a kan mutum.

A hanzarta zuwa asibiti da zarar an kamu da wannan cuta domin samun magani.

7. Dajin dake kama fata.

Likitoci sun ce daya daga cikin alamomin dajin dake kama fata shine yawan jin kaikayi a kai.

Sun ce da zarar an ji kaikayi kuma aka susa sannan kurji ya fito a dalilin haka kamata yayi a garzaya asibiti domin likitoci su duba mutum.

Akan warke daga ciwon daji idan an gano shi da wuri.

Share.

game da Author