Za a ci gaba da kai wa Uzor Kalu albashi da alawus din sa a kurkuku –Majalisar Dattawa

0

Bulalaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Uzor Kalu da aka daure shekaru 12 a kurkuku cikin makon da ya gabata, zai rika karbar dukkannin albashi da alawus-alawus din kudaden da Majalisar Dattawa ke biyan sa.

Za a rika biyan sa wadannan makudan kudaden duk kuwa da cewa ya na daure ba ya zuwa majalisa kuma ba aikin da aka zabe shi ya ke gudanarwa ba.

Kakakin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Godiya Akwashiki ne ya bayyana haka jiya Lahadi ga PREMIUM TIMES.

Ya ce duk da an yanke masa daurin shekarun 12 a kurkuku, har yanzu sanata ne, kuma za a ci gaba da biyan sa albashi da alawus din sa dindi.

Akwashiki ya , “har sai shari’a ta je Kotun Koli, an yanke hukunci na karshe tukunna. Idan Kalu ya yi nasara, zai dawo Majalisa kenan.

Idan kuma bai yi nasara ba, to zai ci gaba da zama kurkuku.”

Sanata Akwashiki ya kara da cewa to daga nan ne za a daina biyan Kalu, sai kuma a sake zaben cike gurbin wanda zai maye kujerar sa.

“Za a ci gaba da biyan sa mana. Ai har yanzu sanata ne. Kuma kotu daya kadai aka je. Idan ya daukaka kara har zuwa Kotun Koli, kuma ya yi nasara, ai shkenan sai ya dawo a matsayin sa na sanata.

“Idan ma Kalu ya daukaka kara, sai Kotun Daukaka Kara ta sake tabbatar da wancan hukuncin shekaru 12 da aka yi masa, to za a ci gaba da biyan sa. Har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe tukunna.” Cewar Akwashiki.

Ya ci gaba da cewa ba a kai wurin da za a fara tallar neman maye Kalu a kan kujerar sa ta sanata ba tukunna.

“Idan ka lura, ko Joshua Dariye ma an rika biyan sa albashi da alawus ya na kurkuku, har sai da karshen zangon Majalisa ta 8 ya kare, sannan aka daina biyan sa.

Share.

game da Author