2020: Gwamnoni 36 sun fara walle-walle da batun karin albashin bai-daya

0

Ganin saura makonni biyu a shiga sabuwar shekarar 2020, wacce ake sa ran daga farkon ta kowace jiha za ta fara amfani da karin albashi, sai ga shi kuma gwamnnin kasar nan su 36 a karkashin Kungiyar Gwamnonin Najeriya, sun fara kame-kamen bayyana kalubalen da ke tattare da fara biyan sabon karin albashi.

A taron da gwamnonin suka yi jiya a sakateriyar su da ke Abuja, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya. Kayode Fayemi, ya shaida wa manema labarai cewa kowane gwamna zauna da kungiyar kwadagon jihar sa, domin ya baje musu komai a faifai dangane da matsalar da za ta shafi jihar sa, idan ya fara biyan karin albashi.

Fayemi ya yi wannan bayani ne, bayan an tambaye shi ko gwamnoni za su ki fara biyan karin albashi, domin babu batun albashi a cikin ajandar taron na jiya Laraba.

Batun biyan naira 30,000 na mafi karancin albashi kuwa, a cewar Fayemi kowane gwamna ya amince zai biya a matsayin mafi karancin albashi.

“To amma inda gizo ke saka shi ne wajen abin da za a kara wa kowane matakin albashi, masu daukar fiye da naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi.”

“Amma tunda jihohin kasar nan ba daidai suke da kowace wajen karfin arziki ba, sai mu ka to kowane gwamna ya je ya tattauna abin da zai iya biya, daidai da karfin jihar sa. Ko yatsun hunnu ma idan ku ka duba ai kun san ba daidai suke ba.”

“Abin da ya fi damun gwamnoni shi ne matsalolin da za a iya fuskanta idan aka kara albashi har zuwa ga mai matakin albashi na 17.” Cewar Fayemi.

“Sannan abin da na sani ne cewa babu wani batu da Kungiyar Gwamnoni ta ta tattauna cewa wai za ta ki biyan naira 30,000 a matsayin karin albashi ga karamin ma’aikaci.

“Ba za mu yi haka ba, amma za mu baje matsaloli da kalubale a fili mu nuna cewa to fa ga abin da za iya fuskanta idan aka ce sai an yi wa masu manyan matakai da mukamai karin albashi.

Share.

game da Author