2019: Mun koyarda matasa 250 sana’o’in hannu – Wassh Waziri

0

Mataimakin shugaban kungiyar Aktocin Najeriya reshen yankin Arewa Maso Yamma, kuma fitaccen dan wasa, kuma Furodusa a farfajiyar fina-finan Kannywood Wassh Waziri Hong ya bayyana cewa kamfanin sa ta koyarda matasa akalla 250 sana’o’in hannu a jihar Kaduna.

Wassh ya bayyana haka ne da yake hira da PREMIUM TIMES a Kaduna.

Wassh ya ce dalilin da ya sa ya maida hankali wajen koyarda matasa sana’o’i shine domin su dogara da kan su.

” Muna yin haka ne domin mu taimaka wa matasa a wannan yanki. Muna koyar dasu sana’o’i domin su iya rike kansu. Bayan sun kammala mukan basu kayan aikin da zasu fara da shi.

Bayan haka Wassh ya ce a matsayin sa na jigo a harkar shirya fina-finan Najeriya, yana da burin ganin an samu hadin kai matuka tsakanin yankin Arewa da Kudu wajen harkar shirya fina-finai.

” Ina son a rika yin fina-finai ta yadda idan ana neman bahaushe a wani fim yayi abu kamar Hausawa, maimakon a saka wani da ba bahaushe ba kaga yana yin abin haka-haka banbarakwai da kuma ko a Kannywood shima idan ana son a saka mutum yayi abu irin na mutanen kudancin Najeriya, kawai sai a dauko dan kudancin kai tsaye, ba sai an yi ta fama da bauhaushe ba. Hakan zai sa a samu hadin kai matuka a tsakanin mu da daukaka a farfajiyar fina-finai a Najeriya.”

” Wani abu da nake so in kira a kai da tunatar da mu shine mu rika hakuri da juna mu dauki wannan sana’a da muhimmanci. Rarrabuwar kai da ake samu a tsakanin manyan jarumai ba zai haifar mana da da mai Ido ba. Wannan ya rika cewa wai shine wane ba abin alfahari bane a garemu. Dole a kowani sana’ akwai na gaba. Kuma dole arika girmama su saboda bautar da suka yi wa sana’ar da ya sa har wasu za su iya tasowa a cikin ta suna tunkaho.

Daga nan sai Wassh ya koka kan yadda masu satar fasaha suka yi wa farfajiyar Kannywood illa matuka da kuma hanyoyin da za su bi domin ceto masana’antar.

” Masu satar fasaha, wato ‘ Piracy’ sun yi wa farfajiyar Kannywood Illa matuka. Yanzu masu shirya fina-finai duk guiwowin su sun yi la’asar saboda babu riba a harkar duk saboda satar fasaha.

” A dakunan Sinima kawai ake nuna fina-finai. Masoyan Kannywood ba su iya shiga wuraren. Suna kokawa da tsada da yayi da kuma rashinsu a wasu jihohin. Hakan ya kawo mana cikas matuka a harkar mu. Sai dai wani abu da zamu mai da hankali a kai shine hada kai da gwamnati wajen yaki da masu satar fasaha. Zamu hada kai mu nuna wa gwamnati yadda za ta taimaka mana sannan da irin amfanin da zata samu musamman wajen kudaden shiga.

A karshe, Wassh ya ce zai ci gaba da maida hankali wajen koyar da matasa sana’o’in hannu da suka hada da koyan shirya fina-finai, hada hotuna, daukan hotuna da dai sauran su.

Share.

game da Author